Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

An fara ƙirga ƙuri'u a Kamaru bayan rufe rumfunan zaɓe na shugaban ƙasa, inda kuma ake sa ran samun cikakken sakamakon a cikin makonni biyu.
Majalisar tsarin mulki wadda ke da alhakin sanar da sakamakon zaɓen tana da kwanaki 15 daga ranar zaɓe kafin ta sanar da sakamakon na ƙarshe.
'Yan ƙasar da ke cikin gida da waje sun kada ƙuri'unsu ga 'yan takara goma da ke neman shugabanci.
Wasu masu sa ido sun ce zaɓen ya gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, duk da cewa an samu ɗan tashin hankali a wasu runfunan zaɓe.
A wani wuri da ke babban birnin Yaoundé, BBC ta hadu da taron masu kaɗa ƙuri'a da ke nuna bacin rai, suna jaddada cewa dole su kare ƙuri'unsu.
Wannan ya faru ne bayan wani jami'in zaɓe ya umarce su da su bar bakin ƙofar ɗakin zaɓen.
A wasu rufunan zaɓen, mutanen da suka fito kaɗa ƙuri'arsu ba su da yawa.
A yankunan da ake magana da Turanci kuma, inda ake samun ɗan tashin hankali saboda ƴan aware sun hana jama'a yin zaɓe, wasu 'yan ƙasa sun fito sun kaɗa ƙuri'arsu, amma kuma da dama sun zauna a gida saboda tsoron harin 'yan bindiga.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan kammala kaɗa ƙuri'a, shugaba Paul Biya ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin nutsuwa, yana cewa an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da nuna dattako na dimokraɗiyya.
Ɗan takara daga jam'iyyar adawa kuma tsohon abokin Biya, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya kaɗa ƙuri'arsa a garinsu na Garoua ya ce an yi masa barazana sosai.
"Ba ni ne matsalar ba," in ji shi ga manema labarai, yana mai ƙara da cewa "na mika kaina ƙarƙashin kariyar Allah da jama'ar Kamaru."
"Ina gidana, kuma ba zan fita ba, ko da a ce suna shirn su zo su kwashe ni daga gidana ne, ba zan motsa ba," in ji shi.
A lokacin yaƙin neman zaɓe, Tchiroma ya tara taron jama'a masu yawa, kuma masana harkokin siyasa sun bayyana shi a matsayin babban mai ƙalubalantar shugaba Biya da ke da shekara 92.
Kafin zaɓen, ministan cikin gida Paul Atanga Nji ya gargadi 'yan takara da su guji ayyana cin nasara da kansu, yana mai jaddada cewa kotun tsarin mulki ce kaɗai ke da ikon fitar da sakamakon hukuma.
Ya ce ya samu rahoto da ke cewa wani ɗan takara wanda ba a bayyana sunansa ba na shirin ayyana kansa a matsayin wanda ya ci zaɓe kafin hukuma ta fitar da sakamako.
Nji ya kuma soki ƙoƙarin wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na tattara sakamakon zaɓe da kansu, inda ya yi barazanar cewa za a kama su kuma a ɗauki matakin doka a kansu.







