Arsenal na iya ɗauko Cunha, Ina Alonso zai tafi?

Cunha

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan gaba na Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, ya ce ya ƙi amincewa da tayin barin Wolves a hunturu amma yanzu ya ce yana son ɗaukar mataki kan makomarsa domin yana son lashe kofuna. (Guardian)

Arsenal na iya ɗauko Cunha, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 62.5, saboda sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta shi ya taimaka wa Atletico Madrid ɗauko ɗanwasan a 2021. (Mail)

Berta ya daɗe yana sha'awar ɗanwasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres kuma ɗanwasan na Sweden mai shekara 26 zai iya dacewa da Arsenal. (Athletic - subscription required)

Ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders ya shiga cikin ƴanwasan da Manchester City ke lissafin ɗaukowa a bazara. (Football Insider)

Ajax na son sake ɗauko ɗanwasan Manchester United da Denmark Christian Eriksen, mai shekara 33 - wanda ya fara taka leda a babbar gasar tamola a Amsterdam. (Manchester Evening News, external)

Everton na shirin ware fam miliyan 25 domin ɗauko ɗanwasan Liverpool da Ben Doak, mai shekara 19, wanda yanzu haka ke taka leda a Middlesbrough a matsayin aro. (Sun, external)

Manchester United na da ƙarin damar ɗauko ɗanwasan gaba na Eintracht Frankfurt Hugo Ekitike saboda ɗanwasan mai shekara 22 na Faransa tun yana matashi shi masoyi ƙungiyar ce ta Old Trafford. (Mirror)

Ana sa ran Bayern Munich ba za ta tsawaita kwangilar ɗanwasan gabanta ba Thomas Muller, amma ɗanwasan mai shekara 35 zai iya komawa taka leda a Amurka. (Sky Sports Germany - in German)

Daraktan wasanni na Bayer Leverkusen Simon Rolfes ya ce Xabi Alonso ya shaida wa ƙungiyar cewa zai ci gaba da aikinsa duk da ana alaƙanta shi da Real Madrid. (Goal)