Real Madrid na shirye-shiryen karawa da Barcelona a Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na shirye-shiryen fafatawa da Barcelona a wasan karshe a Copa del Rey ranar Asabar a Sevilla a filin Estadio La Cartuja.
Ƴan wasan Real Madrid da suka kara da Getafe ranar Laraba, sun yi atisaye a cikin fili da kuma a rufaffen ɗaki ranar Alhamis.
Haka kuma wasu daga cikin ƴan wasan sun motsa jiki su kaɗai daga baya aka raba su zuwa rukunnai, inda suka yi ta wasa da tamaula da bani in baka.
Daga nan aka raba fili gida biyu suka yi amfani da ɓari ɗaya, sun kuma buga shots da fenariti da bugun tazara.
Shi kuwa Alaba ya yi atisaye a rufaffen ɗakin motsa jiki na Real Madrid, an kuma yi atisaye tare da Kylian Mbappe.
Haka kuma ranar Juma'a Real za ta yi atisaye karo biyu, na farko da safe, sannan ta yi na biyu da dare a Estadio La Cartuja a Seville.
Mbappe bai buga wa Real wasan da ta doke Getafe 1-0 ranar Laraba ba, sakamakon jinya, bayan raunin da ya ji a wasa da Arsenal a Santiago Bernabeu.
Barcelona, wadda take ta ɗaya a kan teburin La Liga ta yi nasara a kan Real Mallorca da cin 1-0 ranar Talata.
Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, za ta fuskanci Barcelona karo na uku a gasa a bana.
Ƙungiyar Bernabeu ta yi rashin nasara a gida a hannun Barcelona a La Liga da ci 4-0 ranar 26 ga watan Oktoban 2024.
Haka kuma Real ta yi rashin nasara a wasan karshe a Sifanish Super Cup a hannun Barcelona da ci 5-2 ranar 12 ga watan Janairun 2025 a Saudiyya.
Tuni dai aka yi waje da Real Madrid a Champions League, bayan da Arsenal ta yi nasara 5-1 gida da waje.
Ita kuwa Barcelona ta kai ddaf da karshe a babbar gasar tamaula ta Turai, wadda za ta kece raini da Inter Milan gida da waje.











