AC Milan ta kammala ɗaukar aron Felix daga Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan ƙwallon Chelsea, Joao Felix ya kammala komawa AC Milan, kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.
Ƙungiyar ta Italiya ta biya £5m kuɗin ɗaukar aron Felix, amma ba tare da kulla yarjejeniyar sayar da ɗan wasan ba mai shekara 25.
Koda yake ranar Talata aka kammala ƙulla yarjejeniya, amma tun a ranar Litinin aka cike takardu tsakanin Milan da Chelsea, kafin wa'adin rufe kasuwar ciniki ya cika.
Mai shekara 25 ɗan wasan tawagar Portugal ya buga karawa uku a Premier League a bana, amma yana yin wasanni sosai a sauran gasar kofunan Ingila.
Ya zura ƙwallo bakwai a 2024/25 - ɗaya a wasa da Wolves da biyu a karawa da Panathinaikos da Noah da kuma biyu a FA Cup a wasa da Morecambe.
Felix ya fara tamaula a Benfica daga nan ya koma Atletico Madrid a Yulin 2019 kan £113m a mataki na biyar a tsada a tarihin ƙungiyar.
Ya buga wasannin aro a Chelsea da Barcelona daga baya ƙungiyar Stamford Bridge ta saye shi kan £45m a cikin watan Agusta.
Chelsea tana ta shida a teburin Premier League, amma za ta iya komawa ta huɗu idan ta doke West Ham ranar Litinin a wasan mako na 24 da za su kara.
Milan, wadda take ta takwas a teburin Serie A, za ta kara da Roma a zagayen kwata fainals a Coppa Italia ranar Laraba.
Haka kuma Milan za ta fafata da Feyenoord gida da waje a wasan cike gurbi a Champions League a cikin watan Fabrairu.











