Idan aka ci gaba da zagi na zan bar Man United - Ratcliffe

Jim Ratcliffe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗaya daga mamallakan Manchester United, Sir Jim Ratcliffe ya ce zai bar ƙungiyar idan aka ci gaba da zaginsa, kan yadda ake gunanar da ita.

Mai shekara 72 ya mallaki hannun jarin £1.3bn wato kaso 28.9 cikin 100 a yarjejeniyar da ta kai kamfaninsa, Ineos ya karɓi ragamar gudanar da United.

A watan jiya aka bayar da sanarwar United za ta kara korar ma'aikata a karo na biyu, wadda za ta sallami mutum 200, bayan da ta kori 250 a bara.

Haka kuma za a kara kuɗin kallon wasannin United da zai shafi har da matasa masu shekara kasa da 16 da ƴan fansho, wadanda a baya aka yi wa rangwame.

Ranar Talata Ratcliffe ya sanar da shirin gina wa United sabon filin wasa da zai ke ɗaukar ƴan kalo 100,000 kan £2bn.

Iyalan Glazer ne suka sayi United a 2005, waɗan da suka mallaki kaso mafi tsoka a hannun jarin ƙungiyar Old Trafford.

"Ina nufin, zan iya jurewa na ɗan lokaci," in ji Ratcliffe. "Ban damu da rashin farin jini na ba, saboda na fahimci cewa babu wanda ke son ganin halin da United take ciki, kuma babu wanda yake son shawarar da ya kamata mu yanke a halin yanzu.

''Zan ɗan jure na wani lokaci, domin ni mutum ne kuma daga matsakaita. Amma ba shi da kyau, musamman ga abokai da dangi.

"Don haka, daga ƙarshe, idan har ta kai an ci zarafin dangin Glazer, to, sai in ce, haka ya isa, wani ya zo ya ci gaba da gudanar da United.

United wadda take ta 14 a kasan teburin Premier za ta kara da Leicester City ranar Lahadi a Premier League.

Tuni United ta kai zagayen kwata fainals a Europa League na kakar nan.