''Wasu ƴan United ba su da ƙyau ana biyan wasu albashi fiye da kima''

Ratcliffe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Wasu ƴan wasan Manchester United ''ƙwazonsu bai kai ba'' ana biyan wasu ''albashi fiye da kima'' in ji Sir Jim Ratcliffe.

A wata hira da Ratcliffe ya yi, ya ambaci mai wasan tsakiya, Casemiro da mai cin ƙwallaye, Rasmus Hojlund da mai tsaron raga, Andre Ona da waɗan da aka bayar aro wato Antony da Jadon Sancho.

Ya yi waɗan nan kalaman a BBC kan halin da ya tsinci kai a United da ƴan wasan da ya gada da ɗunbin bashin da ake bin ƙungiyar.

Ratcliffe, wanda ya daɗe yana goyon bayan Manchester United, shi ne shugaban kamfanin da yake sarrafa man fetur da ake kira Ineos.

Mai shekara 72 ya kashe £1.3bn wajen sayen kaso 28.94 cikin 100, hakan ya sa ya karɓi ragamr gudanr da United.

Haka kuma shugaban ya yi bayanai kan halin da United take ciki a Premier League, wadda take mataki na 14 a kasan teburi da fatan ƙungiyar za ta lashe babban kofi zuwa 2028.

Kwana ɗaya tsakani da magoya bayan United suka yi zanga-zanga, Ratcliffe ya yi magana kan matsalolin ƙudi da ƙungiyar ke fuskanta da ta kai ana rage ma'aikata.

Batutuwan da Ratcliffe ya yi hira a kai:

Ya yi magana kan bayar da aron Marcus Rashford zuwa Aston Villa

Sun yi kuskuren marawa Erik Ten Hag baya daga baya aka sallame shi da ɗaukar daraktan wasanni Dan Ashworth, wanda ya bar United wata biyar da fara aiki.

Yadda ya yi imanin United ba ta hanyar komawa kan ganiya

Yadda ya amince Ruben Amorim zai daɗe yana jan ragamar United

Yadda ya yi imanin zai mayar da United ''ƙungiya mafi samun riba a duniya''

Yadda ya tsara gina kasaitaccen filin wasa mafi kayatarwa

Ƙalubalen da ya fuskanta a kakar farko a United

Tausayin magoya baya game da wasu sauye-sauyen da yake ganin ya kamata a yi

Yadda yake ji a ransa kan rashin goyon bayan da ake yi wa tawagar mata ya kasance "rashin adalci.