Waiwaye: Kashe 'yanfashin daji 150 a Kebbi da ƙayyade shekarun shiga jami'a
Kamar kowane mako, wannan maƙala ta yi duba wasu muhimman abubuwa da suka faru a Najeriya a makon da muka yi bankwana da shi.
Jami'an tsaro sun kashe 'yanfashin daji kusan 150 a jihar Kebbi

Asalin hoton, Kebbi State Government
Hukumomi a jihar Kebbi sun ce kimanin 'yanfashin daji 150 ne ake kyautata zaton an kashe a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu cikin daren da ya gabata.
Sojojin ƙasa da na sama sun buɗe wuta ne kan ayarin 'yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura a kan hanyarsu ta zuwa yankin Mariga na jihar Neja mai maƙwabtaka bayan samun bayanan sirri game da zirga-zirgarsu.
Hon Husaini Bena, shi ne shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi inda aka rutsa da 'yanfashin, kuma ya faɗa wa BBC cewa bayanai sun nuna cewa baburan da suka fito sun kai kusan 350.
"Bayanan da muka samu ya nuna cewa sun taru a wani ƙauye mai suna Kawaye kuma suna shirin shiga garin Mariga ko Rijau na jihar Neja," in ji shi.
"Allah ya taimaka babu ko mutum ɗaya da ya rasa ransa, ko ya jikkata a ɓangaren mutanen gari ko kuma jami'an tsaro."
Ya ƙara da cewa bayanan da suka samu sun ce waɗanda suka tsere sun koma inda suka fito bayan janye wasu daga cikin gawawwakin mutanensu.
Gwamnatin Najeriya ta ƙayyade shekarun shiga jami'a

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami'o'in ƙasar.
Ministan ilimin ƙasar, Tunji Alausa ne ya bayyana haka a lokacin taron tsara fitar da guraben karatu na 2025 a ƙasar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Za a shigar da ƙa'idar cika shekara 16 a cikin manhajar hukumar JAMB da ke tantance ƙa'idojin bayar da gurbin karatu.
Haka kuma Ministan ya ce za a yi la'akari da ɗaliban da za su cika shekara 16 ranar 31 ga watan Agustan 2025.
A Najeriya ana samun yawan ƙorafi kan bai wa ƙananan yara guraben karatu a jami'o'in ƙasar, wani abu da masana ke cewa zai shafi fahimtarsu da kuma yadda za su iya jure wa wahalhalun karatun jami'a.
Hari kan fadar Sarkin Kano Sanusi

Asalin hoton, Fadar Sarkin Kano Sanusi
Fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta fitar da sanarwa a ranar Talata tana mai cewa wasu ƴan daba waɗanda ta yi zargin masu goyon bayan sarkin Kano na 15 ne ssun kai hari a Gidan Rumfa da ke Ƙofar Kudu.
Bayanai sun ce ƴan daba ne ɗauke da makamai suka kutsa fadar bayan karya babbar ƙofar shiga gidan tare da jikkata jami'an tsaron da ke bai wa fadar tsaro da kuma lalata wasu motocin jami'an ƴansanda da ke ƙofar gidan.
An dai ce maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da Aminu Ado ke wucewa ta fadar bayan ziyarar ta'aziyya a gidan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Ana kallon wannan lamari a matsayin ci gaba da takun-saƙa da ke tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Yadda kalaman Kashim Shettima suka sake tayar da ƙura kan alaƙarsa da Tinubu

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Kalaman Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima na baya-bayan nan sun sake jawo muhawara kan alaƙarsa da Shugaba Bola Tinubu, wadda ke ci gaba da yamutsa hazon siyasar ƙasar kafin babban zaɓe na 2027.
A ranar Alhamis ne Shettima ya bayyana ƙoƙarin da tsohon Ministan Shari'a Mohammed Bello Adoke ya yi wajen hana tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan cire Kashim ɗin a matsayin gwamnan jihar Borno a 2013.
Bayan kalaman ne kuma wasu suka fara danganta abin da ya faɗa da rikicin siyasar jihar Rivers, inda Shugaba Tinubu ya dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Siminalayi Fubara tare da maye gurbinsa da tsohon soja.
Shettima ya yi bayanin ne yayin bikin ƙaddamar da littafin da Adoke ya rubuta game da wata rijiyar ɗanyen man fetur a Najeriya mai suna "OPL 245: Inside Story of the $1.3 billion Nigerian Oil Block".
Karanta cikakken labarin a nan:
Kashe ƴan banga 70 a jihar Filato
Rahotonni daga jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun ce ƴanbindiga sun kai harin kwanton ɓauna kan wasu ƴan banga tare da kashe aƙalla 70 a wasu ƙauyukan jihar biyu.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa sun gano gawarwaki 56 bayan harin na ranar Litinin.
Sai dai bayanai na cewa akwai wasu ƴan bangar da dama da ba a gani ba, waɗanda ake fargabar sun mutu.
Can ma a ƙauyen Banyun na na jihar, wani mazaunin yankin ya tabbatar da kashe ƴan banga 10.
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma ƙona gidaje da dama da dukiyoyi.
Bayanai na cewa tun bayan da hare-hare suka yawaita a wasu yankunan Wase, aka riƙa gayyato ƴan banga daga wasu yankunan jihar da ma jihar Taraba domin taimaka wa tsaron wasu ƙauyukan yankin.
Adadin mutanen da aka kashe a Najeriya a rabin shekarar 2025 ya zarce na 2024

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da haƙƙin ɗan'adam ta Najeriya ta ce adadin mutanen da aka kashe a watanni shidan farkon wannan shekara ya kai 2,266.
Hukumar ta ce adadin ya zarta na mutanen da aka kashe a irin wannan lokaci cikin shekarar 2024, inda aka kashe mutum 2,194.
Sojojin Najeriya na fafutikar ganin sun tunkari matsalolin tsaro daban-daban da ake fama da su a ƙasar, daga Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, zuwa hare-haren ƴan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar da rikicin ƙabilu da na manoma da makiyaya a arewa maso tsakiya da kuma rikicin ƴan aware a gabashin ƙasar.
Lamari ya yi ƙamari a baya-bayan nan inda aka kashe mutum 606 a watan da ya gabata kacal, ciki har da hare-haren da aka kai a ƙauyukan Yelwata da Dauda a jihar Benue, inda aka kashe kimanin mutum 200.
Jihohin Najeriya tara da za a iya samun ambaliya tara cikin watan Yuli

Asalin hoton, AFP
A ranar Litinin ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya Nimet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu yankunan ƙasar.
Nimet ta kuma gargaɗi mazauna wasu yankunan jihohin arewacin ƙasar tara su zama cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon yiwuwar samun ambaliya.
Jihohin da ake sa ran samun ambaliyar sun haɗa da Jigawa da Yobe da Gombe da Plateau da Bauchi da Nasarawa da Kaduna da Katsina da kuma Kano.
Hukumar ta buƙaci mazauna kwari da waɗanda ke zaune a kusa da koguna a waɗannan jihohi su ɗauki mataki tare da zama cikin shiri.
Tinubu na kitsa yadda zai gurgunta haɗakar 'yanhamayya - ADC

Asalin hoton, X/ADC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, wadda wasu manyan 'yanhamayya a Najeriya suka haɗu a ƙarƙashinta domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 ta yi zargin cewa akwai wasu daga cikin gwamnatin Tinubun da ke neman tarwatsa shirin 'yanhamayyar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na riko kuma kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar a yau Litinin, jam'iyyar ta ADC ta bayyana cewa an gayyaci tsofaffin shugabannin jam'iyyar na jihohi da manyan ƙusoshin kwamitin zartarwarta na jihohin arewa maso gabas da arewa maso yamma wata ganawa ta sirri da manyan jami'an gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ce, ''muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar wannan taron ba wai don tsaron ƙasa ba ne ko kuma samar da zaman lafiya.
Shiri ne na nufin harzuka su da tilasta musu idan ma ta kama a shigar da waɗannan mutane cikin wani ƙirƙirarren shiri na kawo cikas ga haɗakar hamayyyar.
''Wannan ba siyasa ba ce. Wannan zagon-ƙasa ne,'' in ji sanarwar.
Jam'iyyar ta ADC ta ƙara da cewa manufar shirin a bayyane take - ita ce haddasa ruɗani a cikin jam'iyyar, da haramta sabon shugabancin jam'iyyar tare da durƙusar da ita daga hanyar da ta kama ta bunƙasa a matsayin sabuwar fuskar 'yanhamayya.











