Yadda kalaman Kashim Shettima suka sake tayar da ƙura kan alaƙarsa da Tinubu

Kashim Shettima

Asalin hoton, Nigeria Presidency

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Kalaman Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima na baya-bayan nan sun sake jawo muhawara kan alaƙarsa da Shugaba Bola Tinubu, wadda ke ci gaba da yamutsa hazon siyasar ƙasar kafin babban zaɓe na 2027.

A ranar Alhamis ne Shettima ya bayyana ƙoƙarin da tsohon Ministan Shari'a Mohammed Bello Adoke ya yi wajen hana tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan cire Kashim ɗin a matsayin gwamnan jihar Borno a 2013.

Bayan kalaman ne kuma wasu suka fara danganta abin da ya faɗa da rikicin siyasar jihar Rivers, inda Shugaba Tinubu ya dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Siminalayi Fubara tare da maye gurbinsa da tsohon soja.

Shettima ya yi bayanin ne yayin bikin ƙaddamar da littafin da Adoke ya rubuta game da wata rijiyar ɗanyen man fetur a Najeriya mai suna "OPL 245: Inside Story of the $1.3 billion Nigerian Oil Block".

Shettima ya ce Adoke "ya yi namijin ƙoƙari" wajen faɗa wa tsohon shugaban ƙasar na Najeriya cewa ba shi da iko bisa doka na tsige ko da zaɓaɓɓen kansila ballantana zaɓaɓɓen gwamna.

Ofishin mataimakin shugaban ƙasar ya ce wasu ne kawai da ke neman tayar da zaune tsaye suka alaƙanta kalaman da siyasar Rivers, inda ya kare matakin gwamnati na dakatar da gwamnan Rivers ɗin.

"Rahoton ya sauya ma'anar kalaman Shettima ne domin cimma wata mummunar manufa," a cewar wata sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban ƙasar.

"Wannan yanayin na Rivers bai yi daidai da na yankin arewa maso gabas ba a lokacin Jonathan...Matakin Tinubu yana kan doka kuma...yadda 'yanmajalisa na jam'iyyu daban-daban suka amince da shi alama ce da ke tabbatar da hakan."

Mene ne haƙiƙanin abin da Shettima ya faɗa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kashim Shettima ne gwamnan jihar Borno daga shekara 2011 zuwa 2019 ƙarƙashin jam'iyyar ANPP mai adawa, yayin da Goodluck Jonathan ke jagorantar Najeriya a jam'iyyar PDP.

A gefe guda kuma, Mohammed Bello Adoke ne ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnati a lokacin.

Da yake magana yayin ƙaddamar da littafin, Kashim ya yi iƙirarin cewa shi ne "mutumin da gwamnatin Jonthan ta fi tsana" a lokacin, yana mai nuni da satar ɗaliban makarantar Chibok da Boko Haram ta yi, wanda ya jawo wa gwamnatin Najeriya suka daga sassan duniya.

"Shugaba Jonathan ya yi ta tunanin cire wannan gwamnan na Borno [yana nuna kansa], amma Mohammed Adoke ya faɗa masa cewa shugaban ƙasa ba ka da ikon cire zaɓaɓɓen kansila ma ballantana gwamna," in ji Kashim Shettima.

"A lokacin, ya sake neman shawarar wani ƙwararren lauyan a majalisar ministoci Tanimu Turaki SAN, wanda ya ce 'e, mai girma shugaban ƙasa na yarda da abin da abokin aikina ya faɗa.'"

Jim kaɗan bayan yin kalaman ne kuma jaridar intanet ta Peoples Gazette ta ruwaito cewa kalaman na Shettima sun nuna cewa "ya nesanta kansa daga matakin Tinubu na dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan Rivers a watan Maris da ya gabata.

Sai dai matakin Tinubu na dakatarwa ne tsawon wata shida a kan gwamnan da majalisar dokoki ta jihar, ba tsigewa ba kamar yadda jaridar ta bayyana.

Tinubu ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira da "tarzomar da ta jawo karyewar doka da oda" sakamakon rikici tsakanin Gwamna Fubara - ɗan jam'iyyar adawa ta PDP - da tsohon Gwamna Nyesom Wike.

A watan Mayun 2013 ne tsohon Shugaba Jonathan ya sanya dokar ta-ɓaci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa sakamakon hare-haren Boko Haram, amma bai cire ko dakatar da gwamnonin jihohin ba.

Alaƙar Tinubu da Shettima

Mabiya harkokin siyasa sun fara cece ku ce ne kan alaƙar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima tun a watan Yuni bayan da wasu 'yan jam'iyyarsu ta APC suka amince wa Tinubu ya nemi tazarce ba tare da hamayya ba.

Hatsaniya ta ɓarke yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar arewa maso gabas - inda Shettima ya fito - wanda aka yi a jihar Gombe.

An samu ruɗani a taron ne bayan shugabannin APC na yankin sun ambaci sunan Shugaba Tinubu shi kaɗai a matsayin wanda zai yi wa APC takara a zaɓen 2027 ba tare da ambatar mataimakinsa Kashim Shettima ba.

Matakin ya haifar da yamutsi a zauren taron, lamarin da ya sa har ta kai ga ba wa hammata iska, inda wasu suka yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje barazana kafin jami'an tsaro su fitar da shi daga wurin.

"Irin abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na APC a shiyyar arewa maso gabas, manuniya ce ga jam'iyyar APC cewa duk wani yunƙuri na sauya Kashim Shettima na iya jefa jam'iyyar cikin matsala a yankin," in ji Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja.

Shi kuwa Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero na ganin ajiye Kashim Shettima zai yi wa APC mummunan tasiri a zaɓen 2027.

"A gaskiyar magana idan har ba a ci gaba da wannan tafiya da Mataimakin Shugaban Najeriya [Kashim Shettima] ba shakka babu APC za ta iya rasa yankin arewa maso gabas, musamman da ake ƙishin-ƙishin ɗin cewa Tinubu zai ɗauko wanda ba Musulmi ba a matsayin mataimaki," in ji shi.

"Idan har ya yi abin da ake zargi to Musulmai za su ga cewa ya ajiye nasu, idan ba a yi aune ba sai jam'iyyar APC ta rasa yankuna da dama a Najeriya."

Fadar shugaban Najeriya ta ce Tinubu zai zaɓi abokin takara bayan ya karɓi tikitin takarar a hukumance yayin taron jam'iyyar da za a yi nan gaba, amma ba ta ce komai ba game da batun ajiye Shettima.

Sai dai baya ga abubuwa na baya-bayan na da suka faru da ke ɗora ayar tambaya kan alaƙar Tinubun da mataimakinsa, a baya ma an riƙa yaɗa raɗe-raɗin cewa an hana Shettima shiga fadar shugaban ƙasa, wani abu da fadar ta musanta.