Hotunan yadda ruwan sama ya tsayar da lamura a wani birnin India

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruwan saman ya lalata kayayyakin mutane da dama - wani bango ya faɗi a ranar Talata inda ya murƙushe wannan motar
An wallafa

Yanzu wani lokaci ne na shekara da ake tsuga ruwan sama a birnin Mumbai na India da kuma wasu sassan na ƙasar, ruwan saman da ke kawo cikas wurin gudanar da lamuran yau da kullum ga miliyoyin mutane.

Sassa daban-daban na birnin na cike maƙil da ruwan sama mai kamo wa mutum ƙugu, inda sassan birnin ke cikin ambaliya.

Hukumar kula da yanayi ta India ta ankarar da jama'a da sauran gundumomin da ke makwaftaka da birnin, inda hukumar ta yi hasashen za a yi ruwa mai ƙarfin gaske a kwanaki biyar masu zuwa.

Tuni aka tura jami'an hukumar da ke kai agajin gaggawa sakamakon afkuwar bala'i zuwa birnin domin ɗaukar matakai.

An saba da yanayin damina a irin wannan lokaci a Jihar Maharashtra - wanda a nan birnin Mumbai yake.

Damina kuma na da amfani matuƙa ga jama'ar birnin, sakamakon manoma na amfani da lokacin domin noma.

Sai dai masana kan yanayi sun bayyana cewa sauyin yanayi ya kawo cikas wurin hasashe a ƴan shekarun nan.

Dubban mutane na komawa Mumbai da zama a kullum domin neman aiki, lamarin da ya sa ake yawan gine-gine wanda ba a iya sa ido a kai.

Wasu wurare da dama na da tsofaffin kwatoci waɗanda suke jawo ambaliyar ruwa.

A ranar Talata, sabon ministan Jihar Maharashtra, Eknath Shinde ya kai ziyara hedikwatar hukumar agajin gaggawa domin lura da yadda ake ceto mutane, a daidai lokacin da mazauna birnin ke iyo a cikin ruwan da ya yi ambaliya.

A wurare da dama, jiragen ƙasan da ke jigilar jama'a sun samu cikas inda suka jawo zirga-zirgar jama'a ta tsaya cik.

A gundumar Thane, jama'a da dama sun bar gidajensu inda suka koma wani wuri daban sakamakon yadda ruwa ya shiga gidajensu.

Haka kuma kogin Kundalika wanda ke a wajen birnin Mumbai ya cika ya tumbatsa zuwa matakin da zai iya zama barazana.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A duk shekara, ruwan sama na jawo cikas ga mazauna birnin Mumbai
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tuni dama hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta India ta yi hasashen za a samu ruwan sama har zuwa ƙarshen mako
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An bar mazauna birnin na gararamba tsawon sa'o'i sakamakonm yadda ruwan saman ya yi ambaliya ya kuma lalata wurare.
..

Asalin hoton, Getty Images

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jama'a sun ta tafiya cikin ambaliyar domin gudanar da hidimominsu.
Mutane da dama sun ta hijira inda suke neman mafaka sakamakon ruwan da ya shiga gidajensu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama sun ta hijira inda suke neman mafaka sakamakon ruwan da ya shiga gidajensu