Hotunan Afrika na mako daga 9-15 ga watan Satumba 2022

A ranar Juma'a wadannan matan a Afrika ta Kudu yayin da suke murnar bikin al'ada na Ratha Yatra, wanda ya samo asali daga al'adar Hindu game da wasu ababen bauta guda uku da aka dauke daga gidajensu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wadannan matan a Afrika ta Kudu yayin da suke murnar bikin al'ada na Ratha Yatra, wanda ya samo asali daga al'adar Hindu game da wasu ababen bauta guda uku da aka dauke daga gidajensu
An wallafa
Bikin, wanda ya samo asali daga India, shi ne irinsa mafi girma da wata kasa ke gudanarwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bikin, wanda ya samo asali daga India, shi ne irinsa mafi girma da wata kasa ke gudanarwa
 Wata mai wakar coci a Habasha tana  waken bikin sabuwar shekarar Ethiopia a cocin  Lutheran da ke Adis Ababa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mai wakar coci a Habasha tana waken bikin sabuwar shekarar Ethiopia a cocin Lutheran da ke Adis Ababa
A nan kuma mabiyan cocin gargajiya ne ke addu'a a Cocin Bole Medhanialem duk dai a bikin sabuwar shekarar a Habasha

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma mabiyan cocin gargajiya ne ke addu'a a Cocin Bole Medhanialem duk dai a bikin sabuwar shekarar a Habasha
Sai dai yayin da wasu ke gudanar da addu'o'i, wasu kuwa  biki suke yi kamar yadda wannan hoton ya nuna.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai dai yayin da wasu ke gudanar da addu'o'i, wasu kuwa biki suke yi kamar yadda wannan hoton ya nuna.
Nan kuma masu tallar kayan sawa ne a birnin Nairobi, yayin da bikin wayar da kan matasa kan tabin hankali, da ta'addanci, da shan miyagun kwayoyi da sauransu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma masu tallar kayan sawa ne a birnin Nairobi, yayin da bikin wayar da kan matasa kan tabin hankali, da ta'addanci, da shan miyagun kwayoyi da sauransu.
Daya daga cikinsu kenan, Dennis Odhiambo daga Kibera aka kashe masa kudinsa a wannan hoton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daya daga cikinsu kenan, Dennis Odhiambo daga Kibera aka kashe masa kudinsa a wannan hoton
Shi ma Sebastian Thoar, an kashe masa canjinsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shi ma Sebastian Thoar, an kashe masa canjinsa.
Sai dai bayan biki a Nairobi an samu turmutsutsi, a lokacin da mutane da dama su ka yi yunkurin kutsa kai filin wasa na Nairobi don shaidar rantsar da sabon shugaban kasa William Ruto. Akalla mutum takwas ne aka ruwaito sun jikkata a turmutsutsin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai dai bayan biki a Nairobi an samu turmutsutsi, a lokacin da mutane da dama su ka yi yunkurin kutsa kai filin wasa na Nairobi don shaidar rantsar da sabon shugaban kasa William Ruto. Akalla mutum takwas ne aka ruwaito sun jikkata a turmutsutsin.
To amma a cikin filin wasan da aka yi bikin rantuswar an cashe, inda magoya bayan Ruto suka baje sanyen da kaya ruwan dorawa, da ta yi daidai da launinsa a lokacin yakin neman zabe.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, To amma a cikin filin wasan da aka yi bikin rantuswar an cashe, inda magoya bayan Ruto suka baje sanyen da kaya ruwan dorawa, da ta yi daidai da launinsa a lokacin yakin neman zabe.
 A nan kuma na yi tsit a ofishin jekadancin Birtaniya da ke Nairobi ranar Laraba, inda wani ma'aikaci ke tsaye kusa da hoton marigayiya Sarauniya Elizabeth ta II, yayin da sabon shugaba ya zo ya yi ta'aziyya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma na yi tsit a ofishin jekadancin Birtaniya da ke Nairobi ranar Laraba, inda wani ma'aikaci ke tsaye kusa da hoton marigayiya Sarauniya Elizabeth ta II, yayin da sabon shugaba ya zo ya yi ta'aziyya
A Afrika ta Kudu kuwa ranar Juma'a wani mutum ne ke kallon zanen Sarauniya a Johannesburg Club, kwana daya bayan mutuwarta..

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Afrika ta Kudu kuwa ranar Juma'a wani mutum ne ke kallon zanen Sarauniya a Johannesburg Club, kwana daya bayan mutuwarta.
A nan kuma wani yaro ne ke baje albasa a kasuwar birnin Algiers

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma wani yaro ne ke baje albasa a kasuwar birnin Algiers
Nan ma birnin Algiers din ne ranar Litinin, inda wani yaron ke duba litattafai a baje kolin dawowa makaranta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma birnin Algiers din ne ranar Litinin, inda wani yaron ke duba litattafai a baje kolin dawowa makaranta
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan ma wata yarinyar ce a Ivory Coast a gaban allon ajinsu bayan fara karatun sabon zango.
Nan kuma a Dakar ne babban birnin Senegal, inda ake daukar wata yar majalisa hoto gabanin zaman farko da majalisar za ta yi tun bayan hutun da ta tafi, bayan an kammala zaben yan majalisar a watan Yuli.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan kuma a Dakar ne babban birnin Senegal, inda ake daukar wata yar majalisa hoto gabanin zaman farko da majalisar za ta yi tun bayan hutun da ta tafi, bayan an kammala zaben yan majalisar a watan Yuli.