Liverpool za ta fafata da Sparta Prague, Brighton da Roma

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Liverpool za ta fafata da Sparta Prague a zagayen 'yan 16 a gasar Europa Lig, yayin da Brighton za ta ɓarje gumi da Roma.
An haɗa West Ham da Freiburg sai kuma gwarzuwar gasar Premier Scotland Rangers da za ta gwada kwanji Benfica.
Za a fara buga wasan farko a gasar ranar 7 ga wayan Maris, sai wasa na biyu da za a buga a mako na biyu na watan na Maris ranar 14.
Ga cikakken jadawalin yadda wasan zai kasance:
Sparta Prague da Liverpool
Marseille da Villarreal
Roma da Brighton
Benfica da Rangers
Freiburg da West Ham
Sporting Lisbon da Atalanta
AC Milan da Slavia Prague
Qarabag da Bayer Leverkusen










