London za ta mayar wa Najeriya kayanta da aka sace lokacin mulkin mallaka

Gunkin Cif Uwangue a Benin da ‘yan kasuwan Portuguese na ɗaya daga cikin abubuwan da za a dawo wa Najeriya

Asalin hoton, HORNIMAN MUSEUM

Bayanan hoto, Gunkin Cif Uwangue a Benin da ‘yan kasuwan Portuguese na ɗaya daga cikin abubuwan da za a dawo wa Najeriya
An wallafa

Wani gidan ajiye kayan tarihi a birnin Landan ya amince zai mayar wa Najeriya kayayyakin da aka sata daga ƙasar a ƙarni na 19 daga Masarautar Benin.

Gidan kayan tarihi na Horniman Museum ya ce zai miƙa kayan 72 ga gwamnatin Najeriya.

Kayayyakin sun ƙunshi tagullar Benin 12, da kuma makullin shiga fadar sarki.

Hukumar kula da wuraren ajiye kayan tarihi ta Najeriya ce ta miƙa buƙatar mayar mata kayayyakin a cikin watan Janairu.

Gidan tarihin da ke kudancin Landan ya ce ya shawarci mazauna unguwar da masu ziyara da yara 'yan makaranta da malaman jami'a da ƙwararru kan al'adu da masu zane-zane da ke Burtaniya da Najeriya kafin ɗaukar matakin.

"Dukkanin korafin da suka gabatar kan makomar Benin mun gamsu, da kuma bukatar al’umma,” a cewar gidan tarihin.

Shugaban gidan tarihin ya ce hakan shi ne mafi “dacewa da da’a” mayar da kayayyakin.

shekara ta 2022 aka bayyana Horniman a matsayin gidan tarihi mafi shahara a duniya.

Asalin hoton, ANDREW LEE

Bayanan hoto, A shekara ta 2022 aka bayyana Horniman Museum a matsayin gidan tarihi mafi shahara a duniya.

A shekarun baya-bayan nan, an samu karuwan matsin lamba ta fuskar siyasa kan gwamnatocin ƙasashen Turai da gidan adana kayayyakin tarihinsu na su mayar da kayayyakin da suka sace a Afirka.

Wannan ya hada da abubuwan da aka ƙera da haure da wanda aka yi amfani da karafa wajen ƙerawasu na masarautar Benin.

Eve Salomon, shugaban gidan tarihin, ya ce: "Shaidu sun nuna ƙarara cewa waɗannan kayayyakin da karfi aka sace su, kuma tuntubar da muka yi ya goyi-bayan ra’ayinmu cewa akwai rashin dacewa da ɗa’a don haka a mayar da su ga ainihi mutanen da suka mallakesu a Najeriya.

"Gidan tarihin Horniman na farin cikin samun damar daukar wannan mataki kuma muna fatan mu yi aiki tare nan gaba da hukumomin Najeriya wajen dawo musu da irin wadannan kayayyaki masu muhimmanci."

Kayayyakin da Horniman zai dawo da su tsiraru ne cikin irin abubuwan tarihin Najeriya da aka gano a wasu gidan adana kayayyakin tarihi ƙasashen yamma.

A watan da ya gabata, Kwalajen Jesus da ke Cambridge da Jami’ar Aberdeen suka dawo da wasu gumakan tarihin masu sifar zakara da kan sarki.

bbc

Mahukutan Jamus sun kuma dawo da gumaka sama da 1,100 ga ƙasar da ke yammacin Afirka.

Hukumar kula da wuraren ajiye kayan tarihi ta Najeriya ta ce wasu daga cikin kayayyakin masu matukar muhummanc za a adanasu a gidan tarihin Benin sauran kuma ana Legas.

Gidan tarihin Burtaniya ne ya fi riƙe da tarin gumakan masarautar Benin.

Ya ce yana fuskantar takunkumi kan dawo da kayayyakin baki ɗaya daga tanadin dokokin gidan tarihin Burtaniya na shekara ta 1963, da kuma dokar kare abubuwan tarihi da al’adu na 1983 na kasa.