Yadda Afrika ke kokarin dawo da tarihinta

Asalin hoton, Pan African Heritage Museum
A cikin takardun da muke samu daga marubuta daga Afrika, mai tuntuɓa kan harkokin watsa labarai da kuma horaswa wato Joseph Warungu ya yi rubutu kan shirin gina katafaren gidan tarihi a Ghana domin baje kolin tarihin Ƴan Afirka.

Za a samu sabon sauyi ga Ƴan Afrika.
Mutanen Maasai da ake samu a Tanzania da Kenya, da mutanen Himba da ke Namibia da na Somalia da ke kusurwar Afrika da mutanen Zulu da ke Afrika ta Kudu da kuma mutanen Mbenga da ke Yammacin Congo da sauran al'ummomi - da alama suna daf da samun wani sabon matsuguni a Ghama.
Ana kyautata zaton mutanen Afrika sun fara ɗunguma su yi hijira jama'a-jama'a sama da shekara 4,000 da suka wuce, a lokacin da ƴan ƙabilar Bantu masu ɗumbin yawa suka bar kudu maso yammacin Afrika inda suka koma zama a wasu sassa na nahiyar.
Sabbin matafiyan a yanzu za su yi tafiya ne akasin haka.
Kamar waɗanda suka gabace su, ba sa buƙatar takardun biza ko kuma takardun tafiya.
Komawar da mutanen za su yi ba wai mutanen ne za su tashi ba ɗungurumgum, al'adun ne za su koma. Tarihin su ne, da yanayin su.
Sabon wurin a tsaunukan Pomadze yake da ke Winneba. Wurin mai girman kadada 10 da ke ke yankin tsakiyar Afrika wanda ke kusan kilomita 60 daga Accra babban birnin ƙasar.
Wuri ne da zai samu karɓuwa wanda ke da ciyawa a harabar wurin.
Idan komai ya tafi yadda ake so, zuwa Agustan shekara mai zuwa wannan wurin zai samar da gini mai tsawon hawa shida.

Asalin hoton, Pan African Heritage Museum
Wurin da Winneba yake, wanda ta nan ne "ƴan ci rani" za su shiga sabon gidansu a Ghana, yana da nisan kilomita ɗaya daga Cape Coast Castle, wanda wuri ne da a zamanin baya ake tafiya da bayi ƙasashen Turawa domin bauta.
Gidan tarihin wanda har yanzu ana kan gina shi, na da buri ɗaya - tattarawa da faɗin tarihin Afrika ta hanyar amfani da muryoyi da kayayyaki da kuma al'adu.
Waɗanda suka assasa wannan aiki sun ce wannan abu yana da muhimanci domin tsawon lokaci, wasu ne daban suke bayar da labari kan tarihin Afrika.
Sun ce idan wani ya bayar da labarin ka, zai bayar da labarin ne ta yadda ya so domin labarin ya yi armashi.
Wannan gidan tarhin na so ne ya fitar da tarihin Afrika ta hanyar hawa kan abin da ake gani ba a fada a tarihin ba da ke da akwai a Afrika sama da shekara 400.
Gidan tarihi ne da ke so ya koyar ya warkar ya kuma zaburar.

Asalin hoton, Pan African Heritage Museum
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya ce gidan tarihin zai zama gida na dindindin da kuma wurin zama ga duka kayayyakin Afrika da aka sace daga nahiyar, kayayyakin da ake ajiyewa a wasu gidajen tarihi na duniya.
Wannan ne gidan tarihi na baya-baya da ake ginawa a nahiyar, baya ga waɗanda suke a Sengal da Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo da Najeriya, kuma yana zuwa ne a lokacin da ake samun karɓuwar batun da ake yi na kayayyakin tarihin Afrika da aka sace a lokacin mulkin mallaka a mayar da su.
Idan aka kalli yadda aka ƙaddamar da zanen gidan tarihin, gidan tarihin zai zama babban gini da zai tsaya a tsaye kuma za a iya ganin shi daga nesa - wuri na kishin Afrika.
A matsayina na mai kishin Afrika, na shiga na duba yadda zanen gidan tarihin yake.
Da an shiga gidan tarihin, idanuwa za su ci karo da abubuwa masu ƙayatarwa da masu kimiyya a Afrika suka ƙera.

Asalin hoton, AfriKin/Doba Afolabi
Zanen da aka yi mai suna 'Nite Vltron' na nuna yadda wani mawaƙi ke ƙoƙarin amfani da duka iskar da ke cikin huhunsa domin busa mabusarsa.
Bayan nan kuma sai zanen da watra Ba'Amurikiya ta yi mai suna Aisha Tandiwe Bell wadda ta shahara wurin amfani da kimiiyarta don samar da zane.

Asalin hoton, AfriKin/Aisha Tandiwe Bell

Batun tattara tarihin Afrika da haɗa shi wuri guda a wani gidan tarihi ɗaya tilo, an fara wannan tunanin ne tun a 1994.
Wanda ya kawo wannan shawara shi ne Kojo Acquah Yankah, wanda tsohon editan gidan jaridar Daily Graphic ne a Ghana kuma a baya ya taɓa zama ɗan majalisa ya kuma taɓa zama minista a gwamnatin marigayi shugaba Jerry Rawlings.
Ya ce abin da ya ja hankalinsa kan wannan batu shi ne taron da ya je na cika shekara 375 da aka tilasta wa wasu Yan Afrika suka isa Jamestown da ke Virginia na Amurka - wanda a nan aka soma aikin bauta Amurka.
"Sama da mutum 5,000 ne waɗanda asalinsu Yan Afrika ne daga faɗin duniya, inda suka tuna da abin da ya faru," in ji Mista Yankah.
"Wannan ne ya ja hankalina domin ƙirƙirar gidan tarihi na kishin Afrika domin haɗa kan Ƴan Afrika da waɗanda asalinsu Afrika ne da kuma ƙara zaburar da Ƴan Afrika kan cewa mutane ne masu arziki da tarihi."
Amma me ya sa za a kafa wannan tarihi bayan akwai wasu gidajen tarihi a Afrika?
"Akwai ƙasa da gidajen tarihi 2,000 a nahiyar idan aka haɗa da sama da 30,000 a Turai da Amurka," in ji mutumin da ya ƙirƙiro kwalejin koyon aikin jarida ta Afrika da ke Ghana.
"Gidan tarihin yana da muhimmanci sakamakon shi kaɗai ne zai iya tattara tarihin Afrika ya kawo shi a ƙarƙashin inuwa ɗaya."
Babban wanda ya soma zana wannan wuri shi ne James Inedu-George, wanda ɗan Najeriya ne da ya shahara wurin tattara al'adun Afrika da kuma mayar da su zane ko gunki.
Tambarin da aka zaɓar wa gidan tarihin shi ne ƙaho, wanda abu ne na sadarwa da ke alamanta farfaɗowar Afrika.

Asalin hoton, Pan African Heritage Museum
Ana gudanar da wannan aikin gina wannan gidan tarihi ta hanyar samun karo-karo na kuɗi wanda ake sa ran wurin zai lashe dala miliyan 50.
Sai dai waɗanda ke kan gaba wurin tallafa wa wannan wuri irin su Shugaba Nana Akufo-Addo suna ganin ya cancanci a kashe waɗannan kuɗaɗe.












