Kayayyakin tarihi da aka gano na shekara 100 sun kara mana ilimi kan Fir'una Tutankhamun

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
- Marubuci, Daga Ijeoma Ndukwe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Kushewar wani Fir'aunan Masar mai suna Tutankhamun a Luxor na ɗaya daga cikin abubuwan tarihi da masu adana kayan tarihi suka yi a zamanin nan.
Wasu kayayyakin tarihi da aka baje a ɗakin karatu na Bodleian da ke Jami'ar Oxford, an yi bikin cika shekara 100 da gano su wanda wani mai adana kayan tarihi na Masar Howard Carter ya yi da kuma tawagarsa.
Hotunan da mai sana'ar ɗaukar hoto Harry Burton ya ɗauka masu walwali tare da rubutu, da tsare-tsare, da kundin bayanai na ɗakin tarihin Carter sun ƙara wa duniya ilimi kan gano ƙabarin, wanda shi ne sarki na farko da aka sani wanda aka yi wa cikakkiyar jana'iza a tsohuwar al'ummar Masar.
Kazalika, sun ƙalubalanci rawar da Carter ya taka da ta sa ake ganin kamar shi kaɗai ne gwarzo, inda suka nuna gudunmawar da wasu 'yan Masar suka bayar waɗanda ake mantawa da su a lokuta.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Wani yaro ɗan Masar ya tallata wata sarƙa babba mai nauyi da aka ɗauko daga ƙabarin Tutankhamun, abin da ya alamta zamani da kuma tsohuwar Masar.
Daga baya mutane da dama sun dinga iƙirarin cewa su ne yaron, ciki har da Hussein Abd el-Rassul na Gurna, wanda ya taimaka wa tawagar carter - sai dai babu wanda aka tantance daga cikinsu.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Wannan hoton na cikin waɗanda aka fi ba wa fifiko a wurin baje-kolin. Yana nuna mutum biyu da kuma wani yaro suna rushe wani bango don buɗe ƙabarin cikin natsuwa.
Carter ya ambaci ma'aikata 'yan Masar huɗu - Ahmed Gerigar, Gad Hassan, Hussein Abu Awad da Hussein Ahmed Said - sannan ya gode musu a aikin nasa.
Sai dai kuma ba zai yiwu a iya tantance su ba daga cikin hotunan da aka ɗauka.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Dr Daniela Rosenow, wani mai adana kayan tarihi na Masar da aka tattara kayayyakin da shi, ya ce Carter ya ɗauki mutum sama da 50 aiki, amma kuma akwai wasu gwamman ma'aikatan, ciki har da yara a wurin.
Duk da cewa ba a bayyana sunayensu ba, Dr Rosenow ya ce binciken ya ƙalubalanci batun bajintar mutum ɗaya.
"Ta hanyar waɗannan hotunan, muna iya ganin gudunmawar ['yan Masar] mai muhimmanci da ta fayyace ƙarara cewa wannan labarin ɓangare ɗaya ne kawai".

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Wannan na nunawa ƙarara hoton tawagar carter na buɗe ƙofofin kushewar. Carter ya durƙusa yayin da mai taimaka masa Arthur Callender da wani mutum da ba a bayyana ba ɗan Masar ke tsaye a kansa.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Wani likitan tiyata ɗan Birtaniya mai suna Douglas Derry ya fara tsaga jikin Tutankhamun lokacin wata "binciken likitoci" da aka fara ranar 11 ga wataan Nuwamban 1925.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Lulluɓin zinare da ake gani a jikin Tutankhamun da aka alkinta na cikin abubuwa mafiya kyau da aka gano a cikin ƙabarin.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Wani mutum-mutumin Anubis, abin bautar matattu, shi ne maudu'in wannan zanen da Carter ya zaɓa, wanda ya ƙunshi bayanai da gwaje-gwaje.

Asalin hoton, Harry Burton/Griffith Institute, Oxford University
Carter ya kira ɗakin ajiye kayayyaki da ke gabashin farfajiyar ƙabarin da suna "Ma'adana".
A wannan hoton, Burton ya yi amfani da haske don ya ƙirƙiri wani yanayi da gangan don ya nuna kushewar abin bauta Anubis.
Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.