Muhimman lokuta 10 na rayuwar Serena Williams

An wallafa

Bisa nasarorin da ta samu a wallon Tennis, ana kallon Serena Williams a matsayin fitacciyar ƴar wasa. Ba-Amurkiyar ƴar shekara 40 na shirin yin ritaya bayan gasar US Open ta bana, kamar yadda ta rubuta a wani saƙon bankwana a Mujallar Vogue cikin farkon watan nan cewa tana janyewa daga wasanni.

Nasarorin da Williams ta samu - lashe gasar Grand Slam sau 23, makonni 319 a matsayin zakara a duniya da ƙarin wasu kambu 14 sun karfafa matsayinta a matsayin jarumar da ta sauya fuskar wasan mata.

Mun yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwa 10 da suka faru da William a ƙwallon Tennis

1. US Open 1999 - lashe babbar gasar Grand Slam ta US Open

Da alama an ɗauki lokaci tun da aka bayyana lashe gasar Grand Slam da Williams ta yi a matsayin abin mamaki.

Bai kasance ba tun bayan da ta lashe gasartana ƴar shekara 17 a gasar US Open ta 1999.

Iri na bakwai ya nuna ba wai kawai ya nuna gwanintar ta ba ta doke Kim Clijsters, Conchita Martinez da Monica Seles, amma kuma zuciya da mai da hankali a cikin nasara uku a jere bayan koma-baya.

Sai kuma ta yi nasara kan Lindsay Davenport da Martina Hingis - da aka ayyana su na biyu da na farko a duniya - inda ta riƙe lambar yabon da ta daɗe tana burin samu.

2. Indian Wells 2001 - samun galaba kan wariyar launin fata domin doke Clijsters

Fuskantar takaici bayan janyewa daga matakin wasan dab dana ƙarshe da Venus Williams ta yi saboda raunin da ta ji a karawarta da ƴar uwarta a wasan ƙarshe da Kim Clijsters daga Belgium.

Ya haifar da wani yanayi mara daɗi a tarihin ƙwallon Tennis inda Venus da Serena da mahaifinsu Richard suka kai ƙara cewa ƴan kallo na nuna musu wariyar launin fata.

An yi ta yi wa Williams wacce ke shekara 19 a lokacin da 'yan uwanta ihu bayan sun isa kotu, duk da cewa ta yi nasara sau biyu a jere.

Irin kokari da tayi na doke babbar wanda suka buga wasar abu ne na jinjinawa.

3. Wimbledon 2002 - zama ta daya a duniya

Lokacin da Serena ta fara wasa, ta saka a ranta cewa za afi sanin ta a matsayin 'kanwar Venus'.

Sai dai mahaifinta Richard, ya yi hasashen cewa karama daga cikin 'ya'yan nasa za ta fi zama zakakuriya, inda hasashen nasa kuma ya zama gaskiya lokacin da Serena ta fara lashe gasar Wimbledon har sau bakwai.

Bayan doke 'yar uwarta Venus a gasar French Open, Serena ta cire duk wani shakku da ake da ita cewa ba za ta iya fafatawa da 'yayarta ba a wasan tennis.

Daga baya, Serana mai shekara 20 ta zo ta zarce yayar ta Venus inda ta zamanto ta daya a duniya, mataki kuma da ta rike har na wata 11 inda ta kasance ta uku bayan Steffi Graf da kuma Martina Navratilova, wadanda suka rike matakin na tsawon shekara shida.

4. Australian Open 2003 - Nasarar Serena ta farko

Mata shida ne kawai suka taba samun nasarar dukkan kyautuka hudu a lokaci guda, inda Serena mai shekara 21 ta shiga jerin sunayen matan bayan samun nasara a kan yayarta a Melbourne.

Williams ta samu nasarori da dama - inda ta lashe gasar Australian Open a 2003 bayan lashe ta French Open da Wimbledon da kuma US Open a 2002 abu kuma da ya sa aka mata lakabi da 'Serena Slam'.

A yayin wani jawabi, Serena ta kasa boye farin cikin ta, inda ta ce bata taba sammanin hakan ba.

5. Australian Open 2007 - Dawo wa hayyacinta

Shekarun 2000, sun zamanto masu wahala cike kuma da kalubale a rayuwar William.

Lokaci ne da aka kashe babbar yayarta Yetunde Price a wani harin bindiga, da kuma ya kasance lokaci da take fama da raunuka. Serena ta yi kasa da mutum 100 da suka fi shahara a duniya a 2006, inda ta koma Melbourne a matsayin na 81 a duniya.

An yi ta magana kan yadda Serana ta kasance da kuma rashin yin shiri a kan lokaci, sai dai ta baiwa mutane mamaki inda ta zake har zuwa wasan karshe tare da samun nasara.

A lokacin, William ta doke wacce ake kyautata zaton cewa za ta zama ta daya a duniya, Maria Sharapova inda ta samu nasara da ci 6-1 da 6-2 cikin wasa mai sa'a daya da minti uku.

6. London 2012 - Williams ta sami nasarar Golden Slam a wasan da aka buga na mutum daya-daya da mutum biyu-biyu

Duk da cewa Serena Williams ta samu nasarori da dama fiye da wasu 'yan wasa, sai dai akwai wani abu daya da ta rasa ,shi ne kyauta a gasar Olympic.

Wannan abu ne da ya sanya Williams mai shekara 30 jajircewa, wacce kuma ta kwashe tsawon shekarar 2011 tana murmurewa daga wani rauni a kafarta.

"Na dauka cewa idan rayuwa ta ta tennis ta zo karshe, ina da kyautar zinare sannan a yanzu kuma ina da komai,'' a cewar Serena.

Ta kasance cikin ganiyarta inda ta doke Sharapova da ci 6-0 da 6-1 da yin murna ta hanyar taka wata rawa mai kayatarwa.

7. Wimbledon 2015 - sake samun kyautar Serena Slam a karo na biyu

Wani abin burgewa da Serena ita ce farfadowa bayan doke ta.

Bayan wasu kurare a gasar Wimbledon a 2014 da ta yi, wadda kuma ya janyo hankali kanta inda daga baya aka ce tana fama da mura, inda ta koma kan ganiyarta har ma da lashe gasar US Open watanni biyu da suka gabata a lokacin.

Ta samu nasarar ne da ci 6-4 da kuma 6-4 kan 'yar kasar Sifaniya Garbine Muguruza inda nasarar ta kasance kyauta ta 21 da ta samu a wasa mai mutum daya-daya

Bayan haka, Serena ta ci gaba da samun nasarori da dama a rayuwarta.

8. Australian Open 2017 - karya tarihin Graf lokacin da take da juna biyu

Bayan kamo tarihin Steffi Graf na samun nasarar Wimbledon sau 22 a 2016, abin da aka yi ta jira shi ne ko Serena za ta iya shan gaban 'yar kasar ta Jamus.

Hakan bai samu ba lokacin da Karolina Pliskova ta doke ta a wasan kusa da karshe na gasar US Open.

Sai dai ta yi amfani da damar da ta samu a gaba a gasar Australian Open, inda ta samu nasara kan 'yar uwarta Venus da kuma karya tarihin da Graf ta kafa.

9. Indian Wells 2018 - komawa fagen wasa bayan ta kusa rasa ranta lokacin haihuwa

Watanni biyar bayan haihuwar 'yarta Olympia a Satumbar 2017, William ta bayyana cewa ta kusa rasa ranta lokacin da jini ya yanke mata bayan haihuwa ta hanyar tiyata

"Na yi sa'a da ban rasa raina ba,'' a cewar Serena.

William ta jajirce wajen ganin ta farfado da kuma komawa fagen wasa a 2018.

Ta fara fafatawa a Indian Wells bayan komawa buga tennis - inda ta yi rashin nasara a hannun Venus shekara 17 daga wani lamari da ya sanya su kauracewa wasa - inda daga baya suka fafata a wasan karshe na Wimbledon da US Open a shekarar.

Duk da cewa Williams ta yi rashin nasara a dukka wasannin, amma ta koma fagen daga da kuma nuna cewa har yanzu tana daya daga cikin taurarin tennis a duniya.

10. Auckland 2020 - tana ci gaba da kafa tarihi a lokacin da take shiga shekaru arba'in na rayuwarta

Ta hanyar daga hannun ta a sama da sauko da kanta da kuma yin ihu, Williams ta kara nanata abin da muka sani na cewa za ta ci gaba da jajircewa a wasa tennis.

Murnar da Serena ta yi bayan doke Jessica Pegula a gasar Auckland Classic ya kasance na daban a wajenta.

Nasarar kuma ta kasance ta farko da ta samu a matsayin ta na uwa.

Hakan kuma yana nufin cewa William mai shekara 38 ta kasance 'yar wasa ta farko da ta lashe gasar WTA na mutum daya-daya sau hudu a cikin shekaru arba'in.

"Gaskiya an dauki lokaci mai tsawo muna fafatawa a tennis,'' in ji Serena bayan samun nasara.