Barcelona da Granada sun raba maki a La Liga ranar Lahadi

Asalin hoton, Getty Images
Matashin ɗan wasa, Lamine Yamal ya ci wa Barcelona kwallo biyu a wasan da suka tashi 3-3 da Granada a gasar La Liga ranar Lahadi.
Mai shekara 16 shi ne ya fara ci wa masu masukin baki ƙwallo daga baya Ricard Sanchez ya farke daga kwallon da Facundo Pellistri ya bugo.
Daga baya ɗan kwallon Manchester United da ke wasa aro, Pellistri ya ci wa baki na biyu, sai dai Robert Lewandowksi ya farke.
Daga baya Ignasi Miquel ya ci wa Granada na uku, sai Yamal ya farkewa Barcelona.
Da wannan sakamakon kungiyar da Xavi ke jan ragama tana da tazarar maki 10 tsakaninta da Real Madrid ta dayan teburin La Liga.
Kuma Barcelona ta barar da damar rage maki da ke tsakaninta da Girona ta biyun teburi da yanzu biyar ne tsakaninsu.
Rashin kokarin Barcelona a bana ya sa Xavi ya sanar cewar zai bar kungiyar a karshen kakar bana, bayan da ita take da La Liga na bara.
Maki daya Granada ta hada a wasan waje kafin zuwa gidan Barcelona, bayan da Granada ke fuskantar barazanar barin La Liga bayan kakar bana.










