Bayanan hoto, Wata gobara da ta tashi a ƴan katako a tsohuwar kasuwar Fanteka da ke jihar Kaduna, Najeriya, ta yi sanadin ƙonewar rumfuna aƙalla 250 da salwantar dukiya mai ɗumbin yawa.
An wallafa
Bayanan hoto, Shugaban kasuwar, Alhaji Sulaiman Shehu ya shaida wa BBC cewa ibtila'in da ya faru a daren Laraba, ya shafi wani ɓangaren ƴan katako ne a cikin tsohuwar kasuwar ta Fanteka.
Bayanan hoto, Shugaban kasuwar ya ce zuwa yanzu ba a iya tantance abin da ya haddasa gobarar ba.
Bayanan hoto, Sai dai ya bayyana cewa masu gadin kasuwar sun bayyana musu cewa cikin dare sun lura wuta na tashi ta wani ɓangaren kasuwa bayan da aka kawo wutar lantarki.
Bayanan hoto, Shugaban kasuwar ya ce, an yi ƙoƙarin kashe wutar a kan lokaci sai dai yunƙurin bai yi nasara ba.
Bayanan hoto, Ya ce jami'an kashe gobarar da ke kusa da kasuwar "ba su da kayan aiki".
Bayanan hoto, A bayanin da ya yi wa BBC "sun kira jami'an kashe gobara na gwamnatin tarayya waɗanda suka zo suka kashe wutar" daga baya.
Bayanan hoto, Shugaban kasuwar ya ce an kafa kwamiti domin tabbatar da ƙiyasin shagunan da lamarin ya shafa.
Bayanan hoto, Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa kasancewarsu masu ƙaramin ƙarfi.
Bayanan hoto, A Najeriya a duk shekara ana samun gobara a kasuwanni, lamarin da ke janyo asarar ɗumbin dukiyoyi.
Bayanan hoto, Sai dai waɗanda gobarar ta shafa su kan samu tallafi a wasu lokutan, yayin da wasu kuwa gobarar kasuwar kan janyo musu karayar arziki.
Bayanan hoto, Sai dai masu sharhi na nuni da cewa cunkushe hanyoyi a cikin kasuwanni na janyo tsaiko a lokacin kai ɗauki, musamman ga motocin kashe gobara.
Bayanan hoto, Yayin da mahukunta ke ci-gaba da jan hankalin al'umma wajen bin matakan kaucewa samun gobara a kasuwanni, ciki har da kashe wutar lantarki kafin a bar kasuwa.