Amurka mafi noman masara a duniya na fuskantar barazana

\
An wallafa

Manoman Amurka kan shafe dare da rana a gonakinsu, inda suke renonta tun tana karama tare da ci gaba da kula da ita har zuwa lokacin da za ta girma tare da fatan samun damina mai albarka.

Scott Haerr, wanda ke noma eka 4,000 na masarar a duk shekara, ya samu albarkar damina a shekrar da ta gabata a yammacin jihar Ohio.

Yayin da aka samu masara mai kwari a shekarar da ta gabata, yawan masarar da aka shuga a afadin kasar ta ragu da yadda aka saba nomata a kasar.

Tashin farashin taki da karuwar farashin man fetur da ake amfani da shi wajen tayar da injuna, sun haddasa raguwar gonakin da ake noma masarar da eka miliyan 3.4. idan aka kwatantan ta shekarar 2021.

Baya ga wannan farin da aka samu a gonakin da ke yammacin kasar ya kara ta'azzara tashin fasarshin masarar Amurka a kasuwar duniya.

Kwazo gami da aiki da fasahar zamani da manoman Amurkan ke da shi ya taimaka wajen snya ta zama kasa ta farko a duniya da ta fi fitar da masarar zuwa kasuwannin duniya.

A kowacce shekara ana fitar da miliyoyin tan na masara daga kasar zuwa fiye da kasashe 60.

To sai dai da alama kasar ta rasa wannan matsayi na wadda ta fi kowa fitar da masarar a duniya, bayan shafe gomman shekaru a kan wanna matsayi.

Masu saye a China - kasar da tafi kowacce kasa sayen masarar - a yanzu ta daina sayo masarar daga Amurka, saboda tana samun masarar da sauki a wasu kasashen.

A watan Janairu, China na sayen masarar Amurka da kashi 70, kasa da abin da ta sya a shekarar da ta gabata.

Sannan cikin watan Mayu China ta fara sayen masara daga Afirka ta Kudu a karon farko, matakin da ke barazana ga manoman Amurka.

d
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba China ce kadai ta rage yawan masarar da take saya daga Amurka ba, a baya-bayan nan kamfanin dillancin rabarai na Reuters ya ruwaito cewa fitar da masarar da Amurka ke yi zuwa kasashen duniya na raguwa cikin gomman shekaru.

Alal misali kasar Mexico wadda ke sayen masara ta kusan dala biliyan 5 daga Amurkan, ta rage adadin masarar da take saye daga makobciyar tata.

To amm kasa daya tilo da za ta amfana da wannan ita ce Brazil.

Masana sun ce a 'yan shekarun baya-bayan nan manoman Brazil na sauya filayen nomansu zuwa gonakin masara.

Wani karin dama da manoman Brazil suka samu shi ne , za su iya noma masara har sau biyu a shekara guda.

"A shekarar da ta gabata kawai, mun an fitar da masara mai yawan gaske a Brazil, fiye da yadda Amurka ta fitar'', in ji Frayne Olson, masanin harkokin noma a Jami'ar jihar Dakota ta Arewa da ke Amurka.

China ta kara yawan masarar da take saya daga Brazil, kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar cinikayyar masara tsakaninsu.

Akwai dalilai masu yawa da suka sanya China ta raba kafa wajen kasashen da take sayen masarar, kamar yadda Harry Murphy Cruise wani mai sharhi kan harkokin kasuwanci a china.

Ya ce baya ga saukin farashi da take samu a wasu kasashen, karuwar zaman doya da manya tsakaninta da Amurka sun kara tilasta mata rabar kafar.

Mista Cruise ya ce matsalolin da kasashen biyu suka samu kan cinikayyar abubuwan latoroni da batira, ba su ne kadai suka sanya China sauya akalar kasuwancinta da Amurka ba.

"Abun ya wuce haka," in jin Mista Cruise, yana mai cewa China na duba yiwuwar kauce wa matsala kan sayen wasu kayayakin Amurka.

"Abinci da abincin kaji alal misali na daga cikin abubuwan da China ke sayowa daga kasahen ketare," in ji shi.

A nata bangare Amurka, farashin masara ya yi tashin gwauron zabo sakamkon wasu dalilai masu yada da suka hadar da tsadar taki,ga tsadar kayan aiki da iri, matsalar hauhawar farashin kayayaki da ta addabi duniya, da yadda gonaki ke tsada a Amurka.

"Babban abin da ke haddasa bambancin farashin masara tsakanin Amurka da Brazil ko Afirka ta Kudu shi ne yadda gonaki ke tsada a Amurka'', a cewar Frayne Olson.

Farashin eka daya na gona masara a jihar Iowa, jihar da ta fi koacce jiha noman masara a Amurka ya karo da kashi 29 cikin 100 a shekarar 2021, sannan ya kara da kashi 17 a shekara 2022, mataki mafi tsada da ya taba kaiwa a tarihi.

A jihar Illinoise ma wadda ke ta biyu a jerin jihohin da suka fi noma masara a kasar, farashin gonaki ya kai matakin da bai taba kaiwa ba a tarihi cikin shekarar da ta gabata.

To sai dai Scott Haerr wani manomia Amurkan, ya ce sakamakon raguwar farashin taki da na man fetur da ka samau a shekarar da ta gabata ne ya sanya bai rage yawan gonakin da yake nomawa ba.

"Za mu iya farfadowa idan muka dage," in ji shi. ya ce akwai matakin da kasar za ta dauka domin hana Brazil kwace mata kambinta na wadda ta foi kowacce kasa fitar da masarar.