Yadda masu zanga-zanga suka kutsa cikin majalisar dokokin Kenya

Kenya protest

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

An wallafa

Masu zanga-zangar nuna adawa da ƙudirin ƙarin haraji a birnin Nairobi na Kenya sun yi wa majalisar dokokin ƙasar ƙawanya yayin da suka keta shingen ƴansanda da aka kawaye ginin majalisar da shi.

Hotunan da aka watsa kai tsaye a gidajen Talabijin na cikin gida sun nuna ɗimbin masu zanga-zanga suna nufar ginin da ke tsakiyar birnin Nairobi.

Wakilan BBC a wurin sun ce an ji ƙarar harbe-harbe daga jami'an ƴan sanda, kuma bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna wasu mutane da suka jikkata a kusa da harabar majalisar.

Dubun dubatar al'ummar kasar Kenya ne ke gudanar da zanga-zanga a birnin Nairobi tun a safiyar yau Talata a wasu garuruwa da biranen kasar.

Tun da farko dai an ɗage zaman majalisar da ke muhawara kan kudirin a yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

Ƴan majalisar dai sun yi muhawara kan kudirin tun da farko a majalisar amma aka ɗage zaman.

An kwantar da waɗansu a asibiti

Wasu mutum 45 sun jikkata kuma an kai su babban asibitin ƙasa wato Kenyatta National Hospital a Nairobi.

Suna samun kulawar likita da kuma yi wa waɗanda suka samu raunukan da ke buƙatar tiyata aiki, kamar yadda asibitin ya bayyana a shafin X.

"Bakwai daga cikinsu sun kasance mata waɗanda suka samu raunuka daban-daban...ba mu samu labarin mutuwar wani ba a zanga-zangar kawo yanzu."

Ana fargabar mutuwar mutane da dama a artabu tsakanin ƴansanda da masu zanga-zanga.

Kenya protest

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Wani likita ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akalla mutum goma aka kashe kawo yanzu.

Ana tsammanin cewa alkaluman za su iya karuwa yayin da ƴansanda ke ci gaba da artabu da masu zanga-zanga a ciki da wajen majalisar dokokin ƙasar.

Ana iya ganin motocin ɗaukar marasa lafiya ɗauke da mutane da suka jikkata daga kan tituna.