Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabuwar Arsenal: Jesus, Fabio Vieira, Marquinhos da Matt Turner
Cikin watan Agusta za a fara kakar tamaula ta bana, inda Arsenal za ta soma buga gasar Premier League ranar 5 ga watan Agusta, inda za ta ziyarci Crystal Palace.
Kakar da aka kammala Gunners ba ta dauki kofi ba, sannan ta kare a mataki na biyar a teburin Premier League, kenan za ta buga Europa League.
Kawo yanzu Arsenal ta dauki Marquinhos daga Sao Paulo da Fabio Vieira daga Porto da kuma Matt Turner daga New England Revolution.
Haka kuma Gunners ta kammala auna koshin lafiyar Gebriel Jesus daga Manchester City, tana kuma son taya Raphinya daga Leeds United.
Arsenal ta daura damarar ganin ta taka rawar gani a kakar da za a fara a cikin watan Agusta ta 2022/23.
To sai dai wasu na ganin har yanzu Arsenal matsakaitan 'yan wasa take dauka, wadanda za ta dade tana mora.
Tun daga 2019 Gunners ke daukar matasan 'yan kwallo ciki har da Gabriel Martinelli da William Saliba da Nicholas Pepe da Kieran Tierney.
Sauran sun hada da Martin Odegaard da Lokonga da Tavares da Tomiyasu da Ben White da kuma Aaron Ramsdale.
Dukkan 'yan wasan suna da shekarun haihuwa kasa da 25 a lokacin da suka koma taka leda a Emirates.
Idan aka yi la'akari Gunners ta ci gaba da daukar matasan 'yan wasa a bana da suka hada da Fabio Vieira mai shekara 22 daga Porto da Marquinhos mai shekara 18 daga Sao Paulo da kuma Gabriel Jesus mai shekara 25 daga Manchester City.
A kakar 2021/22 Gunners ta kashe miliyoyin kudi wajen sayo 'yan wasa kamar yadda manyan kungiyoyin Turai suka yi.
Saboda haka a bana ma ta ci gaba da yin cefane, domin taka rawar gani a kakar da za a fara cikin Agusta.
Wasu jaridun sun ci gaba da wallafa 'yan wasan da Arsenal ke zawarci da suka hada da Lisandro Martinez daga Ajax da kuma Youri Tielemans daga Leicester.
Arsenal na fatan samun lamba tara mai cin kwallo, bayan da Pierre Aubameyang ya koma Barcelona da Alexandre Lacazette wanda ya koma Lyon.
Dan wasa Saka shi ne kan gaba a yawan ci wa Arsenal kwallo a kakar da ta wuce mai 12 a raga.
Saboda haka Gebriel Jesus zai karbi gurbin cin kwallaye a Gunners, yayin da Martinelli da Marquinhos za su taimaka masa.
A kakar da za a shiga koci, Mikel Arteta yana da zabin 'yan wasa a kasa, bayan da Smith Rowe da Odegaard da Fabio Vieira da Nketiah da kuma Pepe kowanne zai daura damarar taka rawar gani.
Arsenal za ta fuskanci buga gasar Premier League da Europa League da FA Cup da kuma League Cup, daga cikin tana fatan daukar dukkan kofunan ko wasu daga ciki.