Bayern Munich na son Gomez, wataƙila Luiz ya koma Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta nuna sha'awarta a kan dan wasan bayan Liverpool Joe Gomez, Chelsea na tunanin sabunta kwantaragin Conor Gallagher, AC Milan na zawarcin Matty Cash na Aston Villa.
Bayern Munich na zawarcin dan wasan bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 27 (Mirror)
Chelsea na tunanin sake sabon kwantaragin dan wasan tsakiyar Ingila Conor Gallagher, mai shekara 24, wanda Aston Villa da Tottenham ke nema. (Guardian)
AC Milan ta tattauna da Aston Villa kan daukar dan wasan bayan Poland Matty Cash mai shekara 26. (Talksport)
Sai dai farashin fam miliyan 30 da Villa ta sanya na iya kawo cikas a tattaunawar. (Athletic)
Ana shirin nada tsohon kocin Lille da Roma Paulo Fonseca a matsayin sabon kocin AC Milan. (Sky Sports)
Wakilin dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 26, ya tuntubi daraktan wasanni na Barcelona Deco yayin da dan wasan na Brazil ke tantance kungyar da ya kamata ya koma a bazara. (Sports Spanish)
Golan Liverpool da Brazil Alisson, mai shekara 31, ya ki amincewa da damar komawa kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya. (Football Insider)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kocin Manchester United Erik ten Hag na shirin tsawaita kwantiraginsa na tsawon shekaru biyu. (Telegraph)
Tsohon kocin Chelsea Graham Potter da kocin West Brom na yanzu Carlos Corberan ne ke kan gaba wajen neman aikin horar da Leicester City. (Athletic}
Chelsea na tunanin zawarcin dan wasan Bournemouth da Ingila Dominic Solanke, mai shekara 26, a bazarar nan. (HITC)
Ana sa ran Liverpool za ta yi tayin sayen dan wasan Portugal da Benfica Joao Neves mai shekaru 19 a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. (Correio da Manha)
West Ham na zawarcin dan wasan Wolves Max Kilman, mai shekara 27, amma farashin dan wasan na Ingila na iya kaiwa fan miliyan 45. (Mail)
Kazalika Hammers din na sha'awar dauko dan wasan gaban Argentina, Matias Soule, mai shekara 21 daga Juventus. (Fabrizio Romano)
Aston Villa ta fara tattaunawa da Marseille kan yiwuwar siyan dan wasan Faransa Matteo Guendouzi mai shekaru 25. (Football Insider)
Fulham ta shirya kan dan wasan baya na Luton dan kasar Ingila Teden Mengi, mai shekara 22, kuma suna shirin siyan a kalla 'yan wasan baya biyu a bazara. (Standard)
Dan wasan baya na Tottenham dan kasar Ingila Djed Spence, mai shekara 23, yana tattaunawa da kungiyar Genoa ta Seria A kan yarjejeniyar zuwa aro (Football Isider)










