Man United ta yi wa Sancho farashin £40m

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta yi wa Jadon Sancho farashin £40m ga duk ƙungiyar da ke son sayen ɗan wasan tawagar Ingila.

Sancho ya buga wasannin aro a kakar da aka kammala tun daga watan Janairu a Borussia Dortmund, bayan da ya samu rashin jituwa da koci, Erik ten Hag.

Mai shekara 24 ya bayar da gudunmuwar da ya kai Dortmund wasan karshe a Champions League da suka kara a Wembley.

To sai dai ƙungiyar da ke buga Bundesliga ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Real Madrid, wadda ta ɗauki kofi na 15 jimilla.

Sancho ya fuskanci ƙalubale a Old Trafford, wanda aka kasa fayyace masa makomarsa a Manchester United, sakamakon rashin jituwa da kociyan ƙungiyar.

Sai dai BBC ta fahimci cewar United ta yi wa ɗan wasan tawagar Ingila farashin £40m ga duk wadda ke fatan sayen ɗan ƙwallon Ingila.

Dortmund na son sake ɗaukar ɗan ƙwallo a karo na biyu, domin ya kara buga mata wasannin aro, yayin da United ke fatan cefanar da Sancho kai tsaye.

Sancho ya koma United daga Dortmund kan £73m a Yulin 2021, wanda saura yarjejeniyar kaka biyu ta rage masa a Old Trafford.

Ana kuma alakanta ɗan ƙwallon tawagar Ingila da zai koma Juventus da taka leda, mai buga gasar Serie A.