Man Utd ta bi layin masu son Guirassy, Real Madrid da Liverpool da PSG na son Yoro

An wallafa

Manchester United, da Newcastle da kuma AC Milan na neman yi wa West Ham yankan baya a kokarin da take yi na sayen ɗan gaban Stuttgart Serhou Guirassy na ƙasar Guinea. (Football Insider)

Liverpool, da Real Madrid da kuma Paris St-Germain na sha'awar sayen matashin dan bayan Lille Leny Yoro mai shekara 18, na tawagar Faransa ta ƴan ƙasa da shekara 21. (Telefoot daga AS)

Brighton ta kammala cinikin matashin ɗan bayan Argentina Valentin Barco mai shekara 19, daga Boca Juniors a kan kusan fam miliyan 8. (Telegraph)

Ɗan gaban Manchester United Anthony Martial zai yi watsi da duk wani tayi daga ƙungiyoyin Saudi Arabia saboda ya fi son ci gaba da taka leda a Turai inda ake danganta ɗan Faransan da tafiya West Ham, ko Inter Milan ko kuma Fenerbahce . (Caught Offside)

Arsenal da Chelsea za su yi zawarcin matashin ɗan bayan Sporting Lisbon Ousmane Diomande na Ivory Coast mai shekara 20 wanda ke gasar cin kofin Afirka. (Record)

Babu tabbas game da zaman Karim Benzema a Al-Ittihad ta Saudiyya saboda ba a ga tsohon ɗan wasan na Faransa a atisayen ƙungiyar ba kuma sunansa ba ya cikin wadanda za su je atisayen da za ta je sansani a Dubai a lokacin huturu ba. (Marca)

Tottenham, daArsenal da kuma Fulham za su yi gogayya da West Ham a ƙoƙarin da take yi na sayen ɗan gaban Feyenoord Santiago Gimenez na Mexico. (Football Insider)

A ranar Litinin ɗin nan ake sa ran gaya wa Everton da Nottingham Forest cewa sun saɓa dokokin gasar Premier na yawan ribar da ƙungiya ya kamata ta samu na wa'adin shekara uku zuwa watan Yuni na 2023. (The Athletic)

Liverpool za ta sayar da mai tsaron ragarta Caoimhin Kelleher na Jamhuriyar Ireland a kan fam miliyan 20 a bazarar nan kuma za ta nemi maye gurbinsa da Anthony Patterson na Sunderland tsohon golan tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21. (Mirror)

Napoli na sha'awar ɗan bayan Chelsea Trevoh Chalobah na Ingila . (Tuttomercatoweb)

Sheffield United na son ɗan bayan Bournemouth Chris Mepham na Wales mai shekara 26. (Sun)

Za a yi gwajin lafiyar Hannibal Mejbri a Sevilla a makon nan bayan cimma yarjejeniyar bayar da ɗan wasan na tsakiya na Tunisia aro da kuma zaɓin sayensa dindindin da Manchester United. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan tsakiya na Bournemouth Joe Rothwell zai yi gwajin lafiya a Southampton kafin kammala yarjejeniyar tafiya aro har zuwa ƙarshen kakar nan. (Daily Echo)

Southampton na neman ɗan wasan gaba na gefe da za ta karɓa aro a watan nan inda Amad Diallo na Manchester United kuma ɗan Ivory Coast da David Brooks, na Bournemouth ke cikin waɗanda take so. (Givemesport)