Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles ta raba maki da Equatorial Guinea a Afcon 2023
Super Eagles ta tashi 1-1 da Equatorial Guinea a wasanta na farko a rukunin A a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast ke karɓar bakuncin gasa ta 34.
A minti na 36 Equatorila Guine ta fara zura kwallo a ragar Super Eagles ta hannun Iban Salvador.
To sai dai minti biyu tsakani Najeriya ta farke ta hannun Victor Osimhen, wanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye a fafatawar neman shiga gasar.
Dan wasan na Napoli, ya ci wa Super Eagles 10, shi ne kan gaba a wannan bajintar a karawar neman shiga babbar gasar tamaula ta Afirka ta bana.
Najeriya ta barar da damar-makin cin kwallo karo da yawa, ita ma Equatorial Guinea ta yi nata kokarin.
Da wannan sakamakon Ivory Coast ce ta daya a rukunin farko da maki uku, bayan da ta yi nasara a kan Guinea Bissau 2-0 ranar Asabar.
Najeriya ce ta biyu da maki daya iri daya da na Equatorial Guinea ta uku da kuma Guinea Bissau ta hadu mara maki ko daya.
Ranar Alhamis rukunin farko zai kara wasa na bibiyu tsakani
Equatorial Guinea da Guinea-Bissau da na Ivory Coast da Najeriya.
Haka kuma a ranar rukuni na biyu za a yi karawa daya tsakanin Masar da Ghana.
Wasannin da za a buga ranar Litinin 15 ga watan Janairu
- Senegal da Gambia
- Kamaru da Guinea
- Algeria da Angola