Real Madrid ta ci gaba da zama a saman teburin La liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta ci gaba da zama a saman teburin La liga bayan da ta doke Osasuna da ci 4-2 a wasan mako na 29.

Real ta fara cin kwallo ne ta hannun ɗan wasanta na gaba Vincius Junior a minti na 4 da fara wasa.

Sai dai ba a jima ba Osasuna ta farke ta hannun Budimir a minti na 7.

Madrid da ta kai ziyara gidan Osasuna ta ci kwallo ta biyu a raga ta wajen ɗan wasanta na baya Dani Carvajal, inda wasan ya koma 2-1.

Bayan dawowa hutun rabi lokaci, Brahim Diaz ya ci wa Real kwallo ta uku a minti na 61.

Jim kaɗan kuma Vinicius Jr ya ci kwallonsa ta biyu ta huɗu kuma wanda Madrid ta ci Osasuna.

Real ta ci gaba da zama a kan teburin La liga da tazarar maki 10 tsakaninta da Girona da ke matsayi na biyu da maki 62, bayan doke ta da ci 1-0 da Getafe ta yi.