Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta canja lambar rigunan wasu ƴan wasanta a bana
Real Madrid ta sauya lambobin rigunan da wasu 'yan wasanta za su yi amfani da su a kakar tamaula ta 2024/25.
Cikin ƴan wasan Camavinga, wanda ke amfani da 12, zai koma saka lamba shida.
Valverde zai koma saka lamba takwas, wanda keda 15, shi kuwa Tchouameni mai amfani da 18 zai koma saka 14.
Arda Güler, wanda ya saka riga mai lamba 24 a kakar da ta wuce, zai koma saka 15, shi kuwa Vallejo zai yi amfani da 18.
Sabon ɗan wasan da Real ta ɗuka, Kylian Mbappe zai saka lamba tara a Real Madrid, wanda ya yi amfani da 10 a Paris St Germain da tawagar Faransa.
To sai dai Luca Modric ne ke amfani da lamba 10, wanda ya koma Real Madrid da taka leda a kakar 2021 daga Tottenham.
Mbappe zai gaji lamba tara a wajen tsohon ɗan ƙwallon tawagar Faransa, Karim Benzema wanda ya yi kaka 13 a ƙungiyar da cin ƙwallo 353 a wasa 647.
Real Madrid, mai rike da La Liga na bara za ta fara kakar bana ranar 17-18 ga watan Agusta da zuwa gidan Real Mallorca.
Za kuma ta karkare wasan La Liga na 2024/25 da karɓar bakuncin Real Sociedad a Saqntiago Bernabeu ranar 24-25 ga watan Mayun, 2025.
Real za ta fara El Clasico a mako na 11 a Bernabeu ranar 26-27 ga watan Oktoba, sannan ta ziyarci Barcelona a mako na 35 ranar 10-11 ga watan Mayu.
Haka kuma za ta fuskanci Atletico Madrid a mako na takwas a Metropolitano ranar 28-29 ga Satumba, sai wasa na biyu a Bernabeu a mako na 23 ranar 8-9 ga Fabrairu.