Chelsea ta ɗauki Dewsbury daga Leicester City

An wallafa

Chelsea ta kammala ɗaukar Kiernan Dewsbury-Hall daga Leicester City kan £30m.

Tuni ɗan ƙwallon mai shekara 25 ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida da za ta karkare a karshen 2030.

Ranar Lahadi aka kammala cinikin ɗan wasan, wanda ya taimakawa Leicester City bin dokar kashe ƙudi daidai samu ta Premier League.

Zai taka leda tare da tsohon kociyansa, Enzo Maresca, wanda ya koma Chelsea a bana, bayan da ya lashe Championship a Leicester City a kakar da ta kare.

Dewsbury-Hall ya ci ƙwallo 12 ya bayar da 12 aka zura a raga a wasa 44 a lik a kakar da ta wuce.

Shi ne aka zaɓa a matakin ɗan wasan da ya fi yin fice a ƙungiyar a gasar ta Championship.

Ɗan ƙwallon bai yadda ya koma Brighton ba a makon jiya, bayan da ƙungiyar ta yi yunkurin sayensa.

Tun farko Leicester City ta bukaci sayar da ɗan wasan kan £40m, bayan da ba ta sallama tayin da Chelsea ta fara yi ba.