Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a yi hutun shan ruwa a wasannin Premier
Za a yi hutun shan ruwa a lokacin wasannin Premier na wannan makon saboda tsananin yanayin zafi a fadin Birtaniya.
Hukumar kula da yanayi ta kasar ta fitar da gargadin cewa za a yi tsananin zafi a yankunan kudanci da tsakiyar Ingila da kuma wasu sassan Wales.
An yi hasashen zafin zai kai har lamba 37 a ma’aunin selshiyas.
Suma wasannin gasar Lig na Ingila (The English Football League) za a bayar da wannan damar a kowane bangare biyu na wasan kasancewara ana sa ran yanayin zafin ya kai 30 a ma’aunin Selshiyas ko ma sama da haka.
Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Ingila ta bullo da wannan tsari na hutun shan ruwa ne karon farko a lokacin annobar korona a lokacin da aka koma wasannin kakar 2019-20 a tsakiyar watan Yuni.
A yanzu dai tuni yanayin zafi ya karu zuwa sama da lamba 30 a ma’aunin Selshiyar a wasu sassan Birtaniya a wannan makon.
An yi wannan hutun shan ruwa a lokacin wasan Premier tsakanin West Ham da Manchester City ranar Lahadin da ta gabata.
Haka kuma a wasannin cin kofin Carabao ma na dare zagayen farko da aka yi a farkon makon nan, ciki har da wasan Coventry da Bristol an yi wannan hutun.
Kociyan Leicester City Brendan Rogers ya ce zafin yana shafar yanayin wasan kuma abu mafi muhimmanci shi ne mallakar kwallon.
‘’A tsawon minti 90, zai yi tasiri to amma ba yadda za ka yi said ai ka yi iya kokarinka idan yanayin ya zo,’’ in ji shi.