Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Autan ƴar biyat ya buge Ilele a damben Maraba
Autan ƴar biyat ya buge Ilele a damben Marabar Nƴanya da suka kara ranar Lahadi da safe a jihar Nasarawa, Najeriya.
Autan ƴar biyat Guramada ya yi nasara a kan Ilele Garkuwan Mai Caji daga Kudu a turmin farko da suka taka dambe.
Tun farko Ilele ya yi fushi da kin daukar ƙaddara da cewar Autan ƴar biyat ya sa masa kafa ne ba kisa bane.
To amma daga baya an zagaya da dan damben Guramada, bayan da aka tabbatar da cewar an buge Ilele da hannu ba ture ba ne.
An kuma buga dambe da yawa sakamakon ranar ce aka yi wa Inda da Shagon Mada a Marabar Nƴanya.
Wasannin da aka yi kisa:
Bahagon Ali Kansila ya buge Boloko
Lagada ya yi nasara a kan Shagon Terminator
Bahagon Ali Yaro ya doke Shagon Autan Ɗan Bunza
Wasannin da aka yi canjaras:
Aljanin Nokiya da Shagon Sharif
Jan Idon Guramada da Ɗan Yalon Dijango
Mabilu da Shagon Ɗan Aliyu
Bahagon Ali Kansila da Shagon Dunan ba ta jemu ba
Ushu Shagon Inda da Autan na Aisha
Ɗan Sama'ila Shagon Alabo da Autan Fafa
Shagon Kurma da Shagon Inda
Shagon Autan Ɗan Bunza da Sabon Gundumi.