Me ya sa 'yan wasan Premier suka fi jin rauni tsakanin manyan gasar kasashen Turai

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan Premier sun fi jin rauni a tsakanin manyan gasar kwallon kafa na kasashen Turai biyar, kamar yadda wani bincike da aka gudanar a kakar da ta gabata ya nuna.
Cikin 'yan wasan 1,231 da suka ji rauni a Premier, Chelsea ce tafi kowacce kungiya yawan 'yan wasan da suka ji ciwo 97, kamar yadda bincike ya nuna.
Kungiyoyin Ingila sun yi matukar asara dalilin raunin da 'yan wasansu suka ji, wanda ya kai £184.57m.
'Yan wasa 4,810 ne suka ji rauni a manyan gasar kasashen Turai biyar, hakan ya karu da kashi 20 idan aka kwatanta da kakar 2020-21.
Binciken da kamfanin Howden ya gudanar, ya ce asarar da raunin da 'yan wasa ta jawo wa kungiyoyin Turai ya kai £513.23m - wanda ya karu zuwa kashi 29 idan aka kwatanta da na bara.
Paris St Germain ta Faransa ce ta fi ko wacce kungiya biyan masu rauni kudade da suka kai £34.22m.
Real Madrid, wadda ta lashe La Liga da Champions League ita ke da yawan 'yan wasa da ke jinya a fadin Turai su 114, kuma tana biyewa PSG wajen biyan masu jinya kudi £33.95m.
Ya yin da ake samun karin wasanni a nahiyar, binciken ya duba ko wannan kudaden da ake biyansu abu ne mai dorewa ga kungiyoyin.
Howden ya ce kakar 2021-22 ita ce kakar da a karon farko aka samu kudaden da ake biyan 'yan kwallo ya haura rabin biliyan a cikin gasa biyar ta nahiyar Turai, da suka hada da Premier da La Liga da Bundesliga da Ligue 1 da kuma Serie A.
Manchester United na da marasa lafiya (81), Liverpool kuma na da (80) sai Chelsea da ta fi kowa da take da 97 a Premier League, Manchester City na da 67.











