Ƴadda 'yan Ukraine ke koƙarin farfado da harkokin kasuwanci a lokacin ƴaki

.
Bayanan hoto, Shugaban kamfanin G-Mak, Lyubomyr Dykun
An wallafa

Lyubomyr Dykun, ya ce kashi 95 na ma'aikatansa ''sun tafi yin yaƙi''.

Shi ne mamallakin wani kamfanin tsaro mai suna G-mak da ke da cibiya a Ukraine.

Tunaninsa ya kasance iri ɗaya da kamfanin tsaro na Amazong Ring.

Kamfaninsa ya kirkiro da wani abu mai kama da karamar akwati da aka saka wa na’urorin daukar hoto a ciki.

Idan na'urar ta ji motsin wani mutum da ba a san shi ba ko wanda ya zo yin sata, ya kan iya wasa masa hayaki mai sa kwalla.

Taken kamfanin shi ne "Yan Ukraine sun san yadda za su kare kansu".

Sai dai, ƴakin ya janyo babbar matsala wa Dykun. An ɗaiɗaita galibin ma'aikatansa.

"Mun rasa mutum biyar," in ji Dykun lokacin da hawaye ke zuba a idanunsa.

Sake farfado da harkoki a lokacin da ya kamata shi ne babbar matsala, sai dai yin hakan a lokacin ƴaki yana da matukar wahala.

Tayar da bama-bamai da far wa gine-gine da kuma katsewar wutar lantarki na cikin matsaloli da ma'aikata ke fama da shi a Ukraine a halin yanzu.

Wata tawaga ta 'yan Ukraine da ke son sake farfado da harkoki ta kai ziyara zuwa Las Vegas wanda ya kasance babban wuri da masu ilimin fasaha ke taruwa.

Sun ce shirin 'The Consumer Electronics Show', babbar damar ce ta haɗuwa da masu zuba jari daga ƙasashen yamma.

Amma samun zuwa shirin abu ne mai wahala.

.
Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin mutanen da suka kikiro da kamfanin Corner, Artem Dudinskyi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Na dauki tsawon kwana uku kafin zuwa nan," in ji Artem Didinskyi, wani daga cikin mutanen da suka kirkiro da cibiyar haɗa kayan kicin a intanet.

An hana mazan Ukraine 'yan kasa da shekara 60 barin ƙasar, hakan ya sa sai da Artem ya nemi izini daga hukumomin Ukraine kafin zuwa taron.

A gare shi, alamun nemon marasa adadi na Las Vegas sun yi nisa daga aiki a Kyiv – inda ake da wutar lantarki a kodayasuhe.

''A wasu lokutan aiki na ya takaita ga amfani da batirin kwamfuta ta...makonni biyu da suka wuce, ban samu wutar lantarki ba har ta tsawon kwanaki uku," a cewar Artem.

A yanzu yana ganin ya samu mafita na yin ayyukansa. Tashar samar da gas da yake da ita tana amfani da injin bayar da haske.

Yana kuma amfani da ita a ofishinsa don samun wuta. Ita ce hanya kaɗai da Artem yake ganin zai iya yin aiki ba tare da wahala ba.

Ya ce baya fama da zafi a gidansa. ''Ina kwana da kariya ta a kan gadona domin ta taimaka mani wajen jin ɗumi,".

.
Bayanan hoto, Mariana Romaniak, mai aiki da kamfanin Rekava

Mariana Romaniak, tana aiki ne da wani kamfanin ƙere-ƙere.

Tana zama ne kusa da iyaƙar Rasha a garin Sumy. ''Yar uwar ta a bangaren kasuwanci, ta ɗauki mataki mai wahala na cire kamfanin a faɗin Ukraine zuwa birnin Lviv.

"Kana cikin wahala idan har kasuwanci kake yi a Ukraine a yanzu," in ji Mariana.

Ba ya ga bama-bamai da ƙarancin wutar lantarki, Mariana ta ce abu ne mai wahala ga sabbin kamfanoni wajen samun kuɗaɗen gudanarwa.

''Ɗaukacin manyan masu zuba jari da muke da su da kuma sojoji dukkansu na goyon bayan sojoji," in ji ta.

Sai dai ta ce akwai wasu abubuwa masu kyau ga kamfaninta. Mariana ta ce zama a Lviv kusa da iyaƙa da Poland – ya taimakawa harkokinta na kasuwanci.

''Mun fara tunanin cewa watakila abu ne mai kyau gare mu na kasancewa kusa da Tarayyar Turai – saboda za mu iya yin harkoki cikin sauki," a cewar Mariana.

An kirkiro da wani kamfani mai suna eFarm don taimakawa manoman Ukraine amfani da taki a filayensu ta hanyar amfani da na'urar tauraron dan adam.

Kamfanin ya sauya a watanni kalilan da suka wuce – inda yake amfani da fasaha wajen gano nakiya a kasa.

.
Bayanan hoto, Tatiana Gorzey, ta kamfanin eFarm

Tatiana Gorzey da ke aiki a kamfanin na kamfanin eFarm, ta ce an gurɓata kashi 30 na filaye a Ukraine. 'Idan filayen suka kasance masu miliyoyin eka ne, zai zama wahala wajen duba su."

Ga Lyubomyr, shugaban kamfanin G-Mak, ya ce yana koƙarin ganin ya samar da ƙarin jami'an tsaro a kamfanin a Amurka.

Gare shi, shirin CES, babbar dama ce na haɗuwa da masu zuba jari.

Yawancin 'yan tawagar sun nuna jajircewa a fagen ƴakins, inda suke fatan nasara.

Idan suka yi nasara, bayan irin ƙalubale da suka fuskanta tun soma ƴakin, suna kuma da damar nasara a ko’ina ba Ukraine kaɗai ba.