Ukraine ta tuhumi Rasha da aikata 'ta'addancin makamashi'

Ukraine power cuts

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya tuhumi Rasha da abin da ya kira 'ayyukan ta'addanci' ta hanyar gurgunta albarkatun makamashin kasarsa da dakarunta ke yi domin ci gaba da mamaye wasu yankuna.

Mista Zelensky ya ce akalla mutum miliyan 4.5 ne ba su da hasken lantarki bayan da Rasha ta kai wasu jerin hare-hare kan tashoshin samar da lantarki na kasar.

Cikin makonnin da suka gbata, Rasha ta rika kai manya-manyan hare-hare da makamai masu linzami da kuma marsa matuka kan tashoshin samar da makamashi na Ukraine.

Wadannan hare-haren na zuwa ne bayan da jami'an Ukraine ke cewa dakarun Rasha na iya janyewa daga birnin nan na Kherson mai matukar muhimanci da ke kudancin kasar.

Cikin wata guda kacal, Rasha ta lalata tashoshin samar da lantarkin da suka kai daya bisa uku na Ukraine, kamar yadda Shugaba Zelensky ke cewa.

Wannan ya tilasta wa gwamnatin Ukraine ba al'ummar kasar shawarar rage yawan lantarkin da suke amfani da shi. Cikin jawabin da ya saba yi cikin ko wane dare.

Shugaba Zelensky ya ce, "A yau din nan kimanin masu amfani da lantarki mliyan 4.5 ne ska rasa shi baki daya."

Kan batun kwato birni Kherson kuwa, Amurka ta ce a ganinta, dakarn Ukraine na da karfin kwace shi daga dakarun Rasha.

Sai dai Ukraine na cewa har yanzu ana gwabza fada a yankin.

Kwacewa da mamaye birnin Kherson da Rasha ta yi a watan Maris, ya kasance wata babbar nasara gareta, sai dai sojojin Ukraine sun dage sosai kuma matakin ya tilasta wa Rashar sake daukan wasu matakai domin ci gaba da mallakar birnin.