Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta taya Vlahovic, Barca za ta dauki Neves na Wolves
Chelsea ta taya dan kwallon Juventus, Dusan Vlahovic, mai shekara 23, kan fan miliyan 70, domin ta dauka a karshen kakar nan. (ESPN)
Itama Manchester United na fatan sayen Vlahovic, wanda ya fayyace cewar yana kwadayin buga Champions league a badi. (Football Transfers)
Leicester City na shirin tuntubar tsohon kociyan Brighton da Chelsea, Graham Potter kan bashi aikin jan ragamar kungiyar a badi. (Football Insider)
Kociyan Roma, Jose Mourinho na son daukar Youri Tielemans, wanda yarjejeniyarsa a Leicester City za ta kare a karshen kakar nan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Barcelona ta kulla yarjejeniya da eja din ‘yan kwallo kan daukar dan wasan Wolverhampton, Ruben Neves, wanda ake sa ran za a yi musaya da Ansu Fati a kunshin kwantiragin. (Sport - in Spanish)
Aston Villa na duba ko za ta iya daukar aron dan wasan Manchester United, Anthony Martial a karshen kakar nan. (Football Transfers
Crystal Palace na son yin zawarcin dan kwallon Bournemouth, Jefferson Lerma, wanda kwantiraginsa zai karkare a kungiyar da zarar an kammala kakar bana. (Sun)
Nottingham Forest na fatan mallakar Golan Manchester United, Dean Henderson, wanda ke wasannin aro a kungiyar a bana. (Telegraph - subscription required)
Manchester United na tattaunawa da Facundo Pellistri kan mika masa kunshin kwantiragi da zai ci gaba da taka leda a Old Trafford zuwa Yunin 2028. (Fabrizio Romano)
A shirye Manchester City take ta sayar da mai tsaron raga Zack Steffen idan yarjejeniyar da yake buga wa Middlesbrough wasannin aro ta cika. (Sun)