Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Vlahovic da Camavinga da Lingard da Alli da Lo Celso da Eriksen

An wallafa

Arsenal ta shiga wani yanayi a farautar da take yi kan ɗan wasa Dusan Vlahovic mai shekara 21, bayan Juventus ta gabatarwa mai kulob din Fiorentina Rocco Commisso da ta yi mai kwaɓi kan matashin ɗan asalin Serbia. (Times)

A gefe guda kuma ana zargin Vlahovic da yin watsi da kiraye-kirayen da ya ke samu daga mai kulob din Fiorentina Joe Barone bayan Arsenal ta nuna zawarcint kan dan wasan gaban a kungiyar ta Seria A. (Metro)

Liverpool na sanya ido kan yadda za ta iya kasancewa da Eduardo Camavinga a Real Madrid bayan shafe tsawon lokaci tana kwaɗayin ɗan wasan tsakiyar mai shekara 19. (El Nacional - in Spanish)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila Jesse Lingard, mai shekara 29, na son barin Manchester United a wannan watan na Janairu. (Manchester Evening News)

Tottenham ta shirya sayar da ɗan wasanta Dele Alli da kuma Giovani Lo Celso ɗan Argentina, bayan dukkanin 'yan wasan biyu da ke buga tsakiya ba su haska ba a karawar da Antonio Conte ya jagorance su da Chelsea a ranar Lahadi. (Goal)

Spurs na kuma farautar ɗan wasan Lewes' Ollie Tanner a kokarin doke tayin da Brighton ta gabatar kan ɗan wasan mai shekara 19. (Athletic - subscription required)

Brentford na gab da ƙulla yarjejeniyar kwantiragin wata shida da ɗan wasan Denmark Christian Eriksen. (Sky Sports)

Newcastle United na gab da cimma yarjejeniyar sayen ɗan wasan Netherlands mai shekara 25 da ke buga baya Mitchel Bakker daga Bayer Leverkusen. (Mirror)

Arsenal ta amince da sharuɗan da aka gindaya mata kan dauko ɗan wasan aro daga Juventus' zuwa karshen kaka, Arthur Melo, mai shekara 25. (90min)

Liverpool na farautar ɗan wasan Fulham mai shekara 19 da kuma ke yiwa Ingila wasa, Fabio Carvalho. (Fabrizio Romano)

Newcastle na tinkahon samun nasarar saye ɗan wasan Atalanta Duvan Zapata, saboda labarin da ta samu cewa ƙungiyar ta Serie A na shirin ba da aronsa kan £8m. (Mirror via HITC)