Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Ƙarin albashi da kisan da sanƙarau ta yi wa mutum 85 a Yobe
Wannan maƙala ce da ke duba muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata
Gwamnatin Najeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi
Gwamnatin tarayya a Najeriya ta yi wa ma’aikatanta ƙarin albashi da kimanin kashi 25 cikin ɗari zuwa kashi 35 cikin ɗari.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin bukin ranar ma’aikata ta duniya.
A ranar Talata ne wata takarda daga shugaban hukumar kula da albashi ta Najeriya, Ekpo Nta ta tabbatar da ƙarin albashin.
Takardar ta nuna cewa ƙarin albashin zai fara ne daga ranar ɗaya ga watan Janairun 2024.
Kamar akasarin al'umma ƙasar, ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun faɗa cikin mawuyacin hali sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.
Sanƙarau ta halaka mutum 85 a Yobe
Gwamnatin jihar Yobe ta ce sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.
Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.
Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.
NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyatan Najeriya
Hukumar alhazai ta Najeriya Nahcon ta ce a ranar 15 ga watan Mayu ne za a fara jigilar maniyyatan bana zuwa Saudiyya domin sauke farali.
Shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabin buɗe taron masu ruwa da tsaki na farko da hukumar ta shirya a Abuja.
Arabi ya ce kimanin maniyyata 51,000 ne za su gudanar da aikin hajjin bana inda ya ce jiragen da suka samu sahhalewa ne za su yi jigilarsu zuwa ƙasa mai tsarki.
Shugaban hukumar ta Nahcon ya ce hukumar ta yanke cewa a bana, duka maniyyatan Najeriya za su yi aƙalla kwana huɗu a Madina kafin soma aikin hajji.
Akwai 'yan fanshon da ke karɓar 4,000 a wata a Borno - NLC
Ƙungiyar 'yan kwadagon Najeriya reshen jihar Borno ta ce wasu mutanen da suka yi ritaya a jihar har yanzu ana biyansu 4,000 a matsayin kuɗin fanshonsu a wata.
Shugaban ƙungiyar Mista Yusuf Inuwa ne ya bayyana haka yayin bayanin da ya gabatar a bikin ranar ma'aikata na 2024 wanda aka yi a jihar Borno.
Ya nemi a sake duba yadda za a kyautata kuɗin da ake biya domin faranta rayuwar 'yan fanshon.
Hakan na zuwa ne bayan wasu bayanai a shafukan sada zumunta sun kwarmata cewa akwai malaman makarantar jihar ta Borno da ke karɓar albashi ƙasa da 10,000 a wata, ko dayake gwamnatin jihar ta musanta batun, tana mai cewa malaman ba ƙwararrun malamai ba ne.
Ba za mu ɗora wa gwamnatin da ta gabata alhakin gazawarmu ba - Shettima
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu ba za ta ɗora alhakin matsalolin - da riƙa fuskanta bayan karɓar mulki - kan tsohuwar gwamnatin da ta gababa ce su ba.
Yayin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da jaridar '21st Century Chronicle' ta shirya, mataimakin shugaban ƙasar, ya ce wannan shi ne lokaci mafi wahala na riƙe muƙami a Najeriya, sakamakon matsalolin da ake fuskanta a ƙasar.
Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na ɗaukar matakai masu tsauri a ƙasar, don fitar da ita daga halin da take ciki.
'Yan Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, lamarin da ya sa 'yan ƙasar da dama ke ɗora alhakin hakan kan tsare-tsare da manufofin gwamnatin ƙasar.