Juventus za ta fuskanci Messi da Neymar da Mbappe a Faransa

PSG

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar 10 ga watan Agustan 2021 duniyar kwallon kafa ta girgiza, bayan da Lionel Messi ya koma Paris St Germain da taka leda daga Barcelona.

Kowa ya yadda da cewar Messi da Barcelona sun yi auren zobe ba mai raba su, sai dai bayan da kungiyar Camp Nou ta fada matsin tattalin arziki ya zama dole Messi ya bar kungiyar.

Komawar kyaftin din Argentina zuwa Faransa da taka leda, kungiyar ta hada shi wasa da Neymar da Kylian Mbappe domin buga wasanni tare.

A kakar farko ba su taka rawar gani ba, duk da kungiyar ta lashe Ligue 1, 'yan wasan uku sun ci karo da kalubale duk da kwarewar da suke da ita a fannin taka leda.

Rashin kwazon su ya sa Real Madrid ta yi waje da PSG a Champions League a zagayen kungiyoyi 16 a bara, kofin da kungiyar Faransa ba ta taba dauka ba.

Tsohon kociyan PSG, Mauricio Pochettino ya taka rawar gani wajen hada 'yan wasan da ke kungiyar a yanzu haka da ya kamata a bashi lokaci ya nuna kansa.

Kociyan ya dauki salon 4-3-3, inda ya bai wa Messi da Neymar damar gara kwallo daga gefen fili su shigo da ita tsakiya, idan da hali su nemi Mbappe ko su ci kwallo da kansu.

Kafin PSG ta karbi bakuncin Juventus a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Talata, menene ya canji bayan tafiyar Pochettino?

Shin ko daukar sabon koci Christopher Galtier zai bai wa kungiyar samun nasarar lashe kofin Zakarun Turai a bana?

Sabon kocin ya saita 'yan wasan uku a kakar nan

Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Messi da Neymar da Mbappe sun fara kakar bana da cin kwallo 32 da taimaka wa wajen bayar wa a zura a raga a koda yaushe, bayan da kocin ya koma salon taka leeda 3-4-3.

Neymar da Messi sun ci kwallo 22 a tsakaninsu a kakar nan, bayan wasa shida a babbar gasar tamaula ta Faransa, wadanda a bara suka zura 36 a raga a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce.

Yadda mai tsaron baya Sergio Ramos da Marquinhos ke raba kwallo da yadda Presnel Kimpembe ke kai kwallo ga 'yan tsakiya cikin natsuwa, ya sa PSG kan gara tamaula ta kuma mamaye wasa da kaso mafi rinjaye tun daga baya zuwa gaba.

Salon da kungiyar ke takawa a bana ya dace da yadda 'yan wasan gefe daga baya Nuno Mendes da Achraf Hakimi ke taka rawar gani wajen gudu da kwallo zuwa gaba su kuma bai wa wanda ya kamata daga inda ya dace.

Hakan ya kan ba su damar kai kwallo gaban, sannan su dawo tsare gida su kuma taimakawa masu buga tsakiya a PSG a sabon salon da aka dora kungiyar.

Galtier ya gamsu da kwazon da Marco Verratti ke yi daga tsakiya tare da sabon dan kwallon da ta dauka Vitinha, wanda ya taka leda a Wolves a kuma gasar Premier League.

A kalla Verratti kan raba kwallo sau 83 a kowanne wasa shi kuwa Vitinha kan yi sau 52, yadda suke bai wa 'yan baya daga gefe su kuma mikata ga masu cin kwallaye su ukun ya kara fito da kwazon kungiyar.

Wadan nan da ke buga wa PSG tsakiya sun karbi aikin yadda ya kamata domin ba sa barin 'yan gaban su tsaya ba tare da kai musu tamaula ba a koda yaushe.

PSG

Asalin hoton, Getty Images

Hakan ne ya sa aka bai wa Neymar da Messi da Mbappe damar watayawa a fili da suke abin da suka ga ya dace domin kungiyar ta samu nasara a wasanninta.

Daman kowanne gwani ne wajen murza leda wato Messi da Neymar da Mbappe, idan suna tmurza ttamaula a bana, gwanin ban sha'awa.

Koda yake sun dan samu matasala musamman daga Mbappe da ya fara son kai cewar bugun fenariti shi kadai zai ke yi, to amma yanzu an dinki barakar komai ya koma yadda ya dace.

Salon da sabon koci yake yi a yanzu ya bai wa Messi da Neymar da Mbappe taka leda kusa da kusa ba wahalar da juna, hakan ya sa suke raba kwallo a tsakaninsu sannan suke cin kwallaye.

Messi da Neymar kowa ya bayar da kwallo shida-shida aka zura a raga, sune kan gaba a wannan bajintar a dukkan manyan gasar Turai biyar a kakar nan.

PSG tana rukuni daya da Juventus da Benfica da Maccabi Haifa a bana a Champions League..

Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta Faransa za ta fuskanci Juventus a Champions League.

PSG wadda ke fatan daukar kofin Zakarun Turai domin ake sakata cikin sahun manyan kungiyoyin tamaula a Turai za ta yi kokarin ganin ta kai zagayen gaba, wanda tuni masana suka hangi haka.

Juventus da Benfica za su iya bai wa kungiyar ta Faransa matsala, domin sun lashe Champions League a baya sun san dadin kofin.

Saboda haka dama ce ga PSG ta saka kwazo a kakar nan, bayan da 'yan wasanta uku fitattu Messi da Neymar da Mbappe suka kama da wuta a kakar nan.