Mbappe na gaban Haaland a cin kwallaye a Champions League

An wallafa

Kyalian Mbappe shi ne kan gaba a jerin wadanda suka ci kwallaye a Champions League kakar 2022/23 kawo yanzu.

Dan wasan tawagar Faransa yana da shida a raga, bayan da ya ci Maccabi Haifa biyu a wasan da Paris St Germain ta yi nasara da ci 7-2 ranar Talata.

Kungiyoyin sun buga wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai ranar Talata.

Tuni PSG ta kai zagaye na biyu da maki 11, iri daya da na Benfica wadda ta doke Juventus 4-3 a Portugal.

Sauran da ke biye da Mbappe a cin kwallaye a Champions League sun hada da Erling Haaland da Robert Lewandowski da Mohamed Salah da kowanne yake da biyar-biyar.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Champions League a 2022/23

  • Kylian Mbappe Paris Saint-Germain 6
  • Erling Haaland Manchester City 5
  • Frantzdy Pierrot Maccabi Haifa 5
  • Mislav Orsic Dinamo Zagreb 5
  • Robert Lewandowski Barcelona 5
  • Mohamed Salah Liverpool 5
  • Jude Bellingham Borussia Dortmund 4
  • Rafa Silva Benfica 4
  • Leroy Sane Bayern Munich 4
  • Giacomo Raspadori Napoli 4

Haaland shi ne kan gaba a cin kwallo, bayan da ya zura biyu a ragar Copenhagen a wasa na uku a cikin rukuni, amma bai yi karawa ta hudu ba.

Sannan bai zura kwallo ba a raga a wasa da Dortmund a Jamus da City ta tashi 0-0. ranar Talata

Barcelona za ta kara da Bayern Munich, watakila Lewandowski ya yi wani abun, haka ita kuwa Liverpool ta ziyarci Ajax - kila Salah ya kara nuna kansa ranar Laraba.