An ci tarar Guardiola duk da matsin da yake fuskanta

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An ci tarar kocin Manchester City Pep Guardiola duk da cewa yana fama da rashin isasshen barci da cin abin saboda matsalar da aikinsa ke fama da ita.

A wata tattaunawa da ya yi da tsohon ɗan kwallon Italiya Luca Toni a tashar Amazon a ranar Laraba bayan kashin da ya sha a hannun Juventus a wasan Champions, Guardiola ya yi magana kan yadda yake kallon rashin ƙoƙarin da City take yi a yanzu.

Guadiola ya ce ranshi a yanzu kullum a "ɓace" yake, barcinsa ya fuskanci koma baya, kuma baya cin abinci da yawa domin baya narkewa da wuri.

City za ta buga wasan hamayya da Manchester United a ranar Lahadi a Etihad, yayin da ta ci wasa ɗaya tal cikin 10 da ta buga a baya.

Rashin rasanar da ta yi a hannun Juventus na nufin da yiwuwar ta rasa damar buga wasan cike gurbi a Champions.

Da aka ce ya yi bayani kan abubuwan da ya faɗa a hirarsa da Toni sai ya ce, "ƙalau nake".

"Kullum so muke muyi abu mai kyau ko wanda ya fi kyau in da yiwuwa. Idan kuma hakan bai samu ba ka fi shiga damuwa sama kowa, kuma hakan na faruwa ko da yaushe.

"Idan komai na tafiya daidai ina cikin farin ciki, amma idan ya kasance za mu yi wasa na gaba tunanina shi ne mai zan yi ya fi na baya."

Guardiola ya ce dole City ta riƙa kare bayanta a duk lokacin da take wasa."

Domin jaddada abin da yake nufi, Guardiola ya ba da misali da wasan Sporting lokacin da Ruben Amorim ke kocin ƙungiyar, wanda zai jagoranci United a ƙarshen makon nan.

City ce ta mamaye mintina 45 ɗin farko na wasa, ta samu nasarar cin kwallaye ɗaya da farko sannan aka farke aka zura mata kwallo uku cikin minti 11 aka ta shi 1-4.

Idan har City za su samu sauki to sai dai a wajen United da ba ta ƙoƙarin komai.

Nasarar da suka samu a wasan Europa a kan Plzen ita ce ta uku a ƙarƙashin shugaabncin Amorim amma wasa ɗaya ya ci a Premier, ya yi rashin nasara a hannun Arsenal da Nottingham Forest.