Kane ya ci ƙwallo na 29 a wasa na 29 a Bayern Munich a bana

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Celtic ta yi rashin nasara 2-1 a gida a hannun Bayern Munich a wasan cike gurbi zagayen farko a Champions League ranar Laraba.

Bayern ta ci ƙwallon farko ta hannun Michael Olise, sannan Harry Kane ya kara na biyu.

Ƙwallo na 29 da Kane ya zura a raga a bana kenan a Bayern Munich a fafatawa 29, guda bakwai daga ciki a Champions League.

Saura minti 11 a tashi daga wasan ne Celtic ta zare ɗaya ta hannun Daizen Maeda a karawar da suka yi a Celtic Park.

Wannan shi ne wasa na biyar da suka kara a tsakaninsu a Champions League, inda ƙungiyar Jamus ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.

Ranar Talata 18 ga watan Fabrairu, Bayern Munich za ta karɓi bakuncin Celtic a wasa na biyu na cike gurbi a Champions League.

Celtic ta kawo wannan matakin bayan da ta kare a mataki na 21 a teburi, wadda ta ci wwasa uku da canjaras uku da rashin nasara biyu.

Ita kuwa Bayern Munich, wadda ta ci karawa biyar baka doke ta wasa uku ta kammala a mataki na 12.

Wasan da suka fuskanci juna a gasar zakarun Turai:

2024/2025 Champions League Laraba 12 ga watan Fabrairun 2025

  • Celtic 1 - 2 Bayern Munich

2017/2018 Champions League Talata 31 ga watan Oktoban 2017

  • Celtic 1 - 2 Bayern Munich

Champions League Laraba 18 ga watan Oktoban 2017

  • Bayern Munich 3 - 0 Celtic

2003/2004 Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2003

  • Celtic 0 - 0 Bayern Munich

Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2003

  • Bayern Munich 2 - 1 Celtic

Sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba:

  • Club Brugge 2 - 1 Atalanta
  • Celtic 1 - 2 Bayern Munich
  • Feyenoord 1 - 0 AC Milan
  • Monaco 0 - 1 Benfica 1