An ci Tottenham karo na huɗu a jere a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta yi rashin nasara karo na huɗu a jere a Premier League, bayan da Leicester City ta doke ta 2-1 ranar Lahadi.
Leicester wadda aka fara ci tun kan su je hutu, ta farke ta kuma kara na biyu a zagaye na biyu cikin minti huɗu,
Jamie Vardy da Bilal El Khannouss ne suka ci wa Leicester ƙwallaye, hakan ya sa ta kawo karshen rashin nasara bakwai a jere a gasar ta Premier League.
Tottenham ce ta fara cin ƙwallo ta hannun ɗan kasar Brazil, Richarlison tun kan hutu.
Da wannan sakamakon Tottenham wadda ta ci wasa ɗaya daga karawa 11, hakan ya sa ta koma ta 15 a kasan tteburin bana.
Jerin wasa huɗu a jere da aka doke Tottenham:
Premier League Asabar 4 ga watan Janairu
- Tottenham 1 - 2 Newcastle
Premier League Laraba 15 ga watan Janairu
- Arsenal 2 - 1 Tottenham
Premier League Lahadi 19 ga watan Janairu
- Everton 3 - 2 Tottenham
Premier League Lahadi 26 ga watan Janairu
- Tottenham 1 - 2 Leicester
Ita kuwa Leicester City ta yi sama zuwa mataki na 17 a teburi da tazarar maki ɗaya tsakaninta da ƴan ukun karshe.
Leicester City za ta je Everton a Premier League ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu daga nan ta kara da Manchester United a FA Cup a Old Trafford ranar Juma'a 7 ga watan Fabrairu.
Tottenham kuwa za ta buga Europa League ranar Alhamis 30 ga watan Janairu da Elfsborg, sannan ta fafata a gidan Brentford a Premier ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu.











