Za mu iya ajiye kowane ɗanwasa a benci kuma mu yi nasara - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Babban marubucin labarin wasanni
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
A matsayin sabon kocin Manchester United, babu abin da yake buƙata sama da irin wannan nasara ta doke babbar abokiyar hamayya Manchester City har gida.
Lokacin da ya ajiye biyu daga cikin manyan 'yanwasansa - Rashford da Garnacho - tabbas Ruben Amorim ya san za a caccake shi.
Minti biyu da take wasa a filin Etihad kuma ta nuna cewa Amorim zai fuskanci matsala. Amma daga baya komai ya warware.
Amad Diallo ne ya samo finaretin da Bruno Fernandes ya buga kuma ya farke ƙwallon da Gvadiol ya jefa a ragar United minti 36 da fara wasan.
"Ina ganin hakan," inj ji Amorim lokacin da aka tambaye shi ko United ta cancanci ta yi nasara a wasan a filin wasa na Etihad karon farko tun 2021.
"Mun yi aiki tuƙuru. Wannan wasan ya sha bamban da kashin da muka sha a Arsenal. Ban ji alamun da ma za mu yi nasara ba, amma a yau na ji."
Sa ida cikin tattaunawar da ya yi da manema labarai ta minti takwas, maganar 'yanwasa biyu ce ta mamaye zaman: maganar ajiye Rashford da kuma Garnacho.
A cewarsa: "A yau kulob ɗin ya nuna cewa za mu iya ajiye kowane irin ɗanwasa a benci kuma mu iya yin nasara tare."












