Luke Show ya dawo atisaye bayan jinyar watanni uku

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan bayan Manchester United Luke Show ya koma atisaye bayan jinyar da ya yi ta watanni uku.

Dan wasan bayan Ingilan bai buga wasa ba tun watan Fabirairun, ya yi fama da rauni ne a idan sahunsa a farkon watan Agusta.

Ana sa ran zai dawo wasa ne da an dawo daga hutun wasannin ƙasashe a watan Oktoba, amma tsohon kocin ƙungiyar Erik tan Hag ya fuskanci koma baya.

Show ya ji ciwo a cinyarsa a watan Fabirairu abin da ya jawo masa jinya a ƙarshen wasannin Premeir bara.

Yana cikin waɗanda aka zaɓa a tawagar Ingila a ta Euro 2024 wanda suka sha kashi a wasan ƙarshe a hannun Ingila.

Kocin riƙon kwaryar United Ruud Van Nistelrooy ya ce a farkon wannan wata dan wasan bayan ƙungiyar Tyrell Malacia shi ma zai dawo, wanda rabonsa da ya bugawa ƙungiyar wasa tun watan Afrilun 2023 saboda ciwon da ya ji a gwiwarsa.