Madrid na dab da sanar da ɗaukar Arnold, Arsenal na son Gyokeres, Dean zai koma United

Viktor Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Viktor Gyokeres
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ce kan gaba wajen siyan Liam Delap, Nottingham Forest za ta sayi akalla 'yan wasa biyar a bazara, Arsenal da Liverpool na fafatawa kan Dean Huijsen.

Manchester United ce ke kan gaba wajen neman dauko dan wasan Ipswich dan kasar Ingila Liam Deap, mai shekara 22, wanda zai yi farin ciki matuka da komawa Old Trafford a wannan bazarar. (Sky Sports)

Nottingham Forest za ta sayi yan wasa akalla biyar a bazara, inda dan wasan tsakiya na Manchester City James McAtee mai shekaru 22 dan Ingila da dan wasan Ipswich Deap ke cikin wadanda suke nema. (Telegraph)

Arsenal da Liverpool na zawarcin dan wasan bayan Bournemouth dan kasar Sipaniya Dean Huijsen, mai shekara 20, wanda kuma Real Madrid ke zawarcinsa. (Sky Germany)

Huijsen yana mafarkin komawa Real Madrid, amma kungiyoyin Premier uku Liverpool, da Arsenal da Chelsea sun shirya tsaf don jawo hankalin dan wasan da a kan fam miliyan 50 don cimma yarjejeniyar a wannan watan. (Fabrizio Romano)

Dan wasan Bayer Leverkusen na Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 24, yana dab da komawa Liverpool kan fan miliyan 29.5. (Mail)

Real Madrid na dab da sanar da daukar matashin dan wasan baya na kasar Ingila Trent Alexander-Arnold mai shekaru 26 daga Liverpool. (ESPN)

Manchester United ta tattauna da dan wasan gaban Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, kan yiwuwar komawa kungiyar Bournemouth. (Talksport)

Brighton na tattaunawa da tsohon dan wasan tsakiya na Ingila James Milner, mai shekara 29, kan sabon kwantaragi da kungiyar. (Athletic)

Dan wasan Brazil Rodrygo, mai shekara 24, ba ya son sake buga wa Real Madrid wasa saboda yana shirin ficewa daga kulob din a bazara. (Marca Espanya)

Arsenal na son dauko dan wasan gaban Sporting Lisbon dan kasar Sweden Viktor Gyokeres mai shekaru 26, wanda ya kulla yarjejeniya da kungiyar ta Portugal cewa zai iya barin kungiyar idan wata kungiya ta amince ta biya kusan fam miliyan 60. (Mirror)

Kazalika bayan Gyokeres, Arsenal tana zawarcin dan wasan gaban RB Leipzig na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21. (Sky Sports)