Juventus da Pogba za su raba gari daga karshen Nuwamba

Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paul Pogba zai bar Juventus daga ranar 30 ga watan Nuwamba, bayan da suka amince su raba gari a tsakaninsu.

Cikin watan Fabrairu aka dakatar da Pogba shekara huɗu kan laifin shan abubuwan kara kuzarin wasa daga baya aka rage zuwa wata 18.

Wata majiya daga makusanta Pogba ta sanar da BBC cewar ɗan wasan zai koma atisaye a Janairu, wanda zai iya buga wa wata kungiya daga watan Maris ɗin 2025.

Kenan ɗan wasan tawagar Faransa zai iya komawa fagen daga da taka leda daga Janairun 2025.

Kafin a dakatar da Pogba, yana karɓar albashin £6.9m a duk shekara kan yarjejeniyar da ya kamata ta kare a karshen Yunin 2026.

Daga baya an zabtare albashin Pogba zuwa £2,000 a duk wata, sakamakon yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Juventus da ƙungiyar ƴan wasan tamaula.

Pogba wanda ya daɗe bai taka leda ba, ya yi wasa na minti 162 a karawa biyar a kakar 2022/23 da yin minti 51 a sauyin ɗan wasa a bara kafin a dakatar da shi.

Pogba ya fara taka leda daga Manchester United daga nan ya koma Juventus, wanda ya lashe kofin Serie A daga 2012–13, 2013–14, 2014–15, 2015–16.

Haka kuma ya ɗauki Coppa Italia: 2014–15, 2015–16 da Supercoppa Italiana: 2013, 2015

Daga nan ya sake komawa Old Trafford kan wanda aka saya mafi tsada a duniya kan £89m a 2016, kuma a kakar farko ya lashe Europa League da FA Cup.

Pogba ya buga wa Faransa tamaula karo 91 da lashe kofin duniya a 2018 a Rasha.

To amma yawan jin rauni ya hana Pogba yin abin kirki a kaka ukun karshe a Manchester United da ta kai ya sake komawa Juventus.