Amurka ta ƙara sanya wa alƙalan kotun duniya takunkumi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Amurka na ci gaba da sanya takunkumi a kan ma'aikatan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC- saboda abin da ta kira ayyukan kotun da suka saba doka a kan Amurka da Isra'ila.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, shi ne ya sanar da sanya takunkumin a kan masu shari'a na kotun su hudu a ranar Alhamis.

Biyu daga cikin wadannan masu shari'a na kotun hukunta manyan laifukan ta duniya da ke birnin Hague sun bayar da sammacvin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da tsohon babban hafsansa na tsaro Yoav Gallant, haka kuma masu shari'ar biyu sun bayar da umarnin kotun ta gudanar da bincike kan zargin keta haddi da sojojin Amurka suka yi a Afghanistan.

A sanarwar ta Amurka Sakataren harkokin wajen kasar - Marco Rubio ya ce, ''wadannan mutane hudu sun kasance kai da fata a haramtattun ayyukan ICC da kuma matakai marassa tushe a kan Amurka da shakikiyar kawarta Isra'ila.''

Fitar da wannan sanarwa ta Amurka ke da wuta sai kotun ta duniya ta ICC ta mayar da martani - inda ta yi Allah-wadarai da karin takunkumin na Amurka a kan babban mai gabatar da kara na kotun Karim Khan.

A sanarwar, kotun ta ce matakin na Amurka wanda ta kira lalatacce yunkuri ne karara na rashin martaba 'yancin kotun ta duniya wadda ke aiki karkjashin ikon da take da shi daga kasashe mambobi 125 daga dukkanin sassan duniya.

Shi kuwa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya mika dubun godiyarsa ga Amurka bisa kara kakaba wa kotun ta duniya takunkumi.

Ya ce abun da Trump ya yi, ya nuna a shirye yake ya tsaya wa Yahudawa ko ana-ha -maza-ha-mata.

Matakin ya haramta wa alkalan kotun hudu yin balaguro zuwa Amurka, tare da toshe duk wata kadararsu da ke kasar.