Trump ya ƙaƙaba wa kotun hukunta manyan laifuka, ICC takunkumai

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Amurka, Donald Trump ya rattaba hannu kan wata dokar shugaban ƙasa da ta ƙaƙaba wa Kotun Hukunta Laifukan Yaki ta Duniya, (ICC) takunkumi.

Mista Trump ya zargi kotun da kasancewa 'haramtacciya' wadda kuma dukkan matakan da ta ke ɗauka a kan Amurka da ƙawayenta ba su da tushe.

Umarnin na nufin a yanzu Amurka na damar riƙe kadarori ma'aikatan ICC, da hana su shiga Amurka.

Trump ya sanya hannu kan matakin ne a lokacin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke ziyara a birnin Washington.

A watan Nuwamban da ya gabata ne kotun ta ICC ta bayar da sammacin kame Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza, abin da Isra'ila ta musanta.

Kotun ta ICC ta kuma bayar da sammacin kama wani kwamandan ƙungiyar Hamas.

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC kotun duniya ce da ke da ikon gabatar da ƙara a kan kisan kiyashi, laifuffukan cin zarafin bil adama da laifukan yaƙi.

A shekarun baya-bayan nan, ICC ta kuma bayar da sammacin kama shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Ukraine, da shugabannin Taliban da "ke tsananta wa 'yan mata da matan Afganistan" da kuma shugaban sojojin Myanmar kan laifukan da suka shafi musulmin Rohingya.

Fiye da ƙasashe 120 ne mambobin kotun, ciki har da Birtaniya da ƙasashen Turai da dama, amma Amurka da Isra'ila ba mambobin kotun ba ne.

Ƙasar Netherlands - wadda kotun ke da mazauni a can - ta ce ta yi nadamar matakin na Mista Trump.

Ministan Harkokin Wajen Holland Caspar Veldamp ya ce, "Ayyukan kotun na taka rawa wajen yaƙi da rashin hukunta masu laifi."

Wata sanarwa da fadar 'White House' ta fitar a ranar Alhamis, ta zargi kotun ta ICC - da ke birnin Hague - da aikata abin da ta kira "abin kunya wajen daidaita" Hamas da Isra'ila ta hanyar ba da sammaci a lokaci guda.

Trump ya ce matakin da kotun ta ICC ta ɗauka na baya-bayan nan na da ''hatsarin gaske" wanda ya ce yana ƙoƙarin jefa Amurkawa cikin hadari ta cin zarafinsu da kuma yiwuwar kama su".

Sanarwar ta ce "Wannan mummunan hali na yin barazana ga 'yancin Amurka tare da gurgunta muhimman ayyukan tsaron ƙasa da manufofinta na ƙasashen waje da ƙawayenmu ciki har da Isra'ila.''

A matsayinta na wadda ba mamba a kotun ICC ba, Amurka ta sha yin watsi da duk wani mataki da kotun ke ɗauka kan jami'an Amirka ko 'yan ƙasarta.

White House ta zargi kotun ta ICC da sanya takunkumi kan 'yancin kare kai da Isra'ila ke da shi, tare da yin biris da Iran da ƙungiyoyin da ke adawa da Isra'ila.

Kotun ta ICC dai ta ce yunƙurin wani mataki ne na ɗaura yaƙi ga adalci da doka da oda.

A makon da ya gabata ne ɓangaren ƴan majalisar Democrat a majalisar dattawa suka daƙile wani ƙudirin da ke son sanya wa kotun ta ICC takunkumi, inda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Chuck Shumer ya kira ƙudirin da "wanda bai dace ba" kuma mai cike da "matsaloli".

A wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya ƙaƙaba takunkumi kan jami'an ICC da ke binciken ko sojojin Amurka sun aikata laifukan yaƙi a Afghanistan. Kodayake daga baya gwamnatin Shugaba Joe Biden ta dage takunkumin.

An ɗage takunkuman ne a watan Afrilun 2021, bayan da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya bayyana jerin takunkuman da "waɗanda ba su dace ba kuma marasa amfani''.

To sai dai a makonnin ƙarshe na mulkinsa, tsohon shugaban Amurkan, Joe Biden ya soki sammacin da kotun ICC ta yi wa Netanyahu, yana mai bayyana matakin da "abin takaici'', inda ya ce bai kamata a daidata tsakanin Isra'ila da Hamas ba.

Rattaba hannu da Trump na zuwa ne a daidai lokacin ya gabatar da shirin Amurka na "karbe" ikon Gaza, da sake tsugunar da Falasdinawa wasu yankunan duniya.

Wani mataki da shugabannin Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya suka yi tir da shi.

A ranar Alhamis ne shugaba Trump ya jaddada wannan ƙudiri nasa cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

"Isra'ila za ta mika zirin Gaza ga Amurka a ƙarshen yaƙin," kamar yadda ya wallafa, yayin da yake magana kan yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas da a yanzu ke ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya kuma ƙara da cewa shirin zai ƙunshi sake tsugunar da Falasdinawa, kuma ba za a tura sojojin Amurka ba.