Odegaard zai ɗaura ƙyallen ƙyaftin karo na 100 a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta je gidan Fulham, domin buga Premier League wasan mako na 15 da za su kara ranar Lahadi a Craven Cottage.
Idan har Martin Odegaard ya shiga wasan zai zama karo na 100 da zai ja ragamar Gunners a matakin ƙyaftin.
Haka kuma wasa na 163 da mai shekara 25 zai yi wa Gunners, tun bayan da ya koma Emirates da taka leda daga Real Madrid.
Odegaard ya fara ɗaura ƙyallen ƙyaftin ɗin Arsenal a wasa da Southampton a cikin watan Maris a 2022.
Cikin ƙididdigar da aka yi, ɗan kasar Norway, an ci wasa 66 tare da shi a matakin ƙyftin a Arsenal cikin fafatawa 99.
Hakan ya sa yana kan gaba a yawan nasara a tarihin waɗanda suka yi wa Gunners Gunners ƙyaftin da ya haɗa da Tony Adams da Patrick Vieira da Thierry Henry da kuma Mikel Arteta.
Martin zai zama na biyar a jerin ƙyaftin ɗin Arsenal da suka ja ragamar karawa 100 tun daga 1989, bayan Adams da Vieira da Per Mertesacker da kuma Laurent Koscielny.
Arsenal tana mataki na uku da maki 28, iri ɗaya da na Chelsea, wadda take ta biyu, ita kuwa Fulham mai maki 22 tana ta shidan teburin Premier na bana.
Wasan da aka buga a bara tsakanin Fulham da Arsenal a Premier
Premier League Lahadi 31 ga watan Disamba 2023
- Fulham 2 - 1 Arsenal
Premier League Asabar 26 ga watan Agusta 2023
- Arsenal 2 - 2 Fulham












