Masu gidajen burodi za su fara yajin aiki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wata kungiyar masu gidajen burodi a Najeriya ta ce za ta fara yajin aiki saboda tsadar kayan da ake bukata wajen yinsa.
Kungiyar ta Master Bakers and Caterers ta ce mambobinta a fadin kasar ne za su shiga yajin aikin wanda zai fara daga gobe Alhamis.
Ishaq Abdul-Raheem, shugaban kungiyar reshen Abuja, ya ce sun dade suna daurewa bisa tunanin cewa farashin kayan zai sauka sai dai har yanzu yana ci gaba da tashi.
Ya ce "Fulawa ta yi tsada, suga ya yi tsada, man dizel ya yi tsada, mutane da dama sun rufe kamfanoninsu saboda babu riba.”
Ya kara da cewa masu sana’ar suna asarar hatta uwar kudin da suka zuba a cikinta.
A cewa “Duka ‘yan kungiyarmu da ma wadanda ba su cikin kungiyarmu za su shiga wannan yajin aikin.”
Ishaq ya shaida wa BBC cewar za su fara yajin aikin amma ba su san lokacin da za su tsayar da shi ba, har sai zuwa lokacin da kungiyar ta ga ya dace.
Yaya tsadar kayan hada burodi a yanzu?

Ishaq Abdul-Raheem ya ce tashin farashin ya samo asali ne tun daga lokacin annobar korona.
Ya ce a cikin kwanakin nan farashin kowane buhun fulawa ya karu da kudi Naira 2,000.
An kuma samu karin Naira 1,100 a kan farashin kowane buhun suga.
A cewarsa man dizel wanda a baya suke saya a kan kudi Naira 310, a yanzu ya koma Naira 880 a kan kowace lita.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da masu sana’ar hada burodin za su shiga yajin aiki ba a Najeriyar.
Sai dai a kwanakin nan masu sana’ar sun yi ta kokawa kan hauhawar farashi babu kakkautawa na kayan hada burodin a fadin kasar.
Ishaq ya ce masu sana’ar tasu sun dade suna daurewa, to amma yanzu lamarin ya yi kamari.









