Rayo da Real Madrid sun raba maki a La Liga ranar Lahadi

Vinicius Junior

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Rayo Vallecano da Real Madrid sun tashi 1-1 a wasan mako na 25 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi a Estadio de Vallecas.

Minti uku da take leda Real ta ci ƙwallo ta hannun Joselu daga baya Rayo ta farke ta hannun Raul De Tomas a bugun fenariti.

Kungiyoyin biyu sun kara a wasan farko a bana ranar 5 ga watan Nuwambar 2023 a La Liga, inda suka tashi 0-0.

Real ta karasa wasan na ranar Lahadi da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Daniel Carvajal jan kati.

Real Madrid ce ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta La Liga da maki 62 da tazarar maki shida tsakaninta da Girona ta biyu.

Ita kuwa Rayo, wadda ta ci wasa biyar da canjaras 10 aka doke ta fafatawa 10, tana ta 14 teburin La Liga da maki 25.

Ƴan wasan Real Madrid da suka je gidan Rayo:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Diego Pineiro.

Masu tsaron baya: Carvajal, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García da Jacobo.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Arda Güler.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.

Wasu sakamakon wasannin mako na 25 a gasar La Liga

Ranar Asabar 17 ga watan Fabrairu

  • Atletico Madrid 5-0 Las Palmas
  • Osasuna 2-0 Cadiz
  • Celta Vigo 1-2 FC Barcelona
  • Valencia 0-0 Sevilla

Ranar Lahadi 18 ga watan Fabrairu

  • Rayo Vallecano 1-1 Real Madrid
  • Granada da UD Almeria
  • Real Mallorca da Real Sociedad
  • Real Betis da Deportivo Alaves

Ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu

  • Athletic Bilbao da Girona