Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta ci Union Berlin da ƙyar da gumin goshi
Real Madrid ta ci Union Berlin 1-0 a wasan farko na da suka buga a gasar Champions League a filin wasa na Santiago Bernabeu ranar Laraba.
Daf da za a tashi wasan ne, Jude Bellingham ya ci wa Real ƙwallon, wanda shi ne ƙwallo na shida a kakar nan, idan an haɗa da biyar da ya ci a La Liga.
Jude Bellingham ya zama ɗan wasa na shida daga Ingila da ya buga wa Real Madrid ko dai gasar European Cup ko kuma ta Champions League.
Sauran sun haɗar da Laurie Cunningham da Steve McManaman da David Beckham da Michael Owen da kuma Jonathan Woodgate.
Bellinhgam mai shekara 20, shi ne mafi ƙuruciya daga cikinsu da ya buga wasannin.
Wannan shi ne karon farko da Union Berling ta fara buga gasar, inda ta haɗu da Real Madrid mai riƙe da kofin zakarun Turai 14 jimilla.
Ranar 3 ga watan Oktoba ne, Real Madrid za ta ziyarci Napoli, yayin da Union Berlin za ta karɓi baƙuncin Braga.
Real Madrid tana ta ɗaya a kan teburin La Liga na kakar nan, bayan ta lashe duk wasa biyar da ta kara inda ta samu maki 15.
Ita kuwa Union Berlin tana mataki na takwas a kan teburin Bundesliga da maki shida daga karawa huɗu.
'Yan wasan Madrid da suka kara da Union Berlin:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Cañizares.
Masu tsare baya: Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da Tobias.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma Ceballos.
Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim da kuma Gonzalo.